Gwamna Ya Feɗewa Tinubu Gaskiya, Ya Faɗa Masa Halin da Ya Jefa Ƴan Najeriya

Gwamna Ya Feɗewa Tinubu Gaskiya, Ya Faɗa Masa Halin da Ya Jefa Ƴan Najeriya

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ɗora laifin halin ƙuncin rayuwar da ake ciki kan manufofin gwamnatin Bola Tinubu
  • Sanata Bala ya ce tsare-taren tattalin arziƙi na gwamnatin APC ne ya kawo ƙunci, yunwa da wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki
  • Gwamnan ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta gane cewa matsalar na tattare da ita kuma ta ɗauki matakin canji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a ranar Laraba ya ce manufofin shugaban kasa da jam’iyyar APC ne suka jefa ‘yan Najeriya cikin ƙunci.

Sakamakon haka gwamnan ya yi kira ga shugaban ƙasa da ya soke wasu daga cikin tsare-tsare da mnufofinsa domin tsamo mutane daga wahala.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi darasin da ya kamata gwamnonin Arewa su dauka kan zanga zanga

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnan Bauchi ya ɗora laifin halin ƙuncin da mutane ke ciki kan manufofin Bola Tinubu Hoto: Sen Bala Mohammed
Asali: Twitter

Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin APC ta hanyar manufofinta na tattalin arziki, "ta kara haifar da ƙunci, yunwa, da fushi ga 'yan kasa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan dalilan ne suka tunzura matasa suka fito kan tituna zanga zanga, kamar yadda Tribune Online ta tattaro.

Gwamna Bala ya faɗi kuskuren Tinubu

Gwamnan ya faɗi haka ne a lokacin da yake kaddamar da kamfen PDP da miƙa tutoci ga ‘yan takara a zaben kananan hukumomin jihar nan mai zuwa.

"Shugaban kasa ba ya sauraren gwamnoni waɗanda su ke kusa da talaka, mun fi kusa da jama'a, a koda yaushe muna mutunta al'umma musamman abin da suke so.
"Zanga-zangar nan ta koya mana darasi da dama, ya bayyana a fili cewa gwamnatin APC ta gaza."

Abubuwan da suka kawo wahala

Gwamna Bala ya ƙara da cewa alamu sun nuna tsare-tsaren gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu sun gaza taɓuka komai sai kara jefa mutane cikin wahala.

Kara karanta wannan

Bayan Mangal, wani gwamna a Arewa ya sa hannu a fara aikin gina kamfanin siminti

A rahoton Daily Trust, Bala Mohammed ya ce:

"Ya kamata su fahimci cewa tsare-tsaren gwamnatin tarayya ba sa aiki, duk matsalar daga gare su take, ya kamata su gane manufofinsu ne suka jawo waɗan nan matsalolin."

Gwamna ya fara gina kamfanin siminti

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fara aikin gina masana'antar siminti.

Bala Mohammed ya rattaɓa hannu kan yarjejeniyar MoU da kamfanin Resident Cement Factory Limited na fara gina masana'antar a farkon 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262