Gwamna Ya Cire Tsoro, Ya Faɗawa Tinubu Gaskiya Kan Jawabin Zanga Zangar da Ya Yi

Gwamna Ya Cire Tsoro, Ya Faɗawa Tinubu Gaskiya Kan Jawabin Zanga Zangar da Ya Yi

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya caccaki jawabin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan zanga-zangar da ake yi
  • Ƙauran Bauchi ya ce gaba ɗaya jawabin shugaban ƙasar bai da wata ma'ana ko matakin warware tsadar rayuwar da ake ciki
  • Sanata Bala Mohammed ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta daina ba ƴan Najeriya uzuri, ta yi abin da ya dace kawai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya caccaki jawabin da shugaban kasa Bola Tinubu y yi game da zanga-zangar da ake yi.

A jawabinsa na ranar Lahadi, Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zanga su dakata, su bude kofar tattaunawa, yana mai cewa babu gudu babu ja da baya a cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: A karshe, Ganduje ya yi magana, ya tura sako ga 'yan Najeriya

Gwamna Bala Mohammed Bauchi.
Gwamnan Bauchi ya soki jawabin da Bola Tinubu ya yi ga masu zanga-zanga Hoto: Sen. Bala Mohammed
Asali: Facebook

Channels tv ta tattaro cewa yayin da yake jawabi a wurin buɗe kamfen PDP na zaɓen kananan hukumomi ranar Laraba, Bala Mohammed ya soki jawabin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan jihar Bauchi ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta daina ba ‘yan Najeriya uzuri game da halin da ake ciki.

Gwamnan Bala ya soki jawabin Tinubu

"Na saurari jawabin shugaban kasa da kunnen basira kuma da zuciya ɗaya, amma a zancen gaskiya bai yi wata magana mai ma'ana ba.
"Bai ma aminta da halin da ake ciki ba, kuma bai yi magana kan matsaloli da kalubalen da ake ciki ba. Matsalar ba ta shi ba ce shi kaɗai, duka shugabanni tun daga matakin ƙasa zuwa ƙananan hukumomi."
"Arewa ya kamata mu farka, mu gina shugabanci nagari da mutunta jama’a. Mutane sun kai wuya ga yunwa, dole ne mu magance matsalolin da suka hana mu ci gaba."

Kara karanta wannan

Betta Edu za ta koma kujerar minista? Tinubu ya yi muhimman sauye sauye a ma'aikatar jin ƙai

- Bala Muhammad

Ƙauran Bauchi ya ƙara da cewa tsare-tsaren gwamnatin tarayya sun gaza.

Gwamnan yake cewa kamata shugaban ƙasa da muƙarrabansa su gane matakansu ne suka jefa jama'a cikin wahala, Guardian ta rahoto.

Ministan Tinubu ya caccaki gwamnan PDP

A wani rahoton ministan raya Neja Delta ya zargi gwamnan jihar Edo da sauya buhunan shinkafar da gwamnatin tarayya ta turo a rabawa talakawa.

Abubakar Momoh ya ce gwamnoni da dama sun ɓoye buhunan shinkafar da aka ba su domin su rabawa masu karamin ƙarfi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262