Masu Zanga Zanga Sun Ƙara Yin Ɓarna, Sun Kai Hari Sakatariyar Jam'iyyar APC
- Masu zanga-zanga da ake zargin ƴan daba ne sun yi kaca-kaca da sakatariyar APC da ke titin Fatakwal zuwa Aba a jihar Ribas
- Mukaddashin shugaban APC na jihar Ribas, Cif Tony Okocha ya ce sun san waɗanda suka ɗauki nauyin wannan aika-aika
- Okocha ya ce wasu manyan mutane ne suka turo ƴan daban domin suna jin haushin yadda APC ke kara yaɗuwa a jihar Ribas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Ƴan daban da ake zargin suna fakewa da zanga-zanga sun farmaki sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Ribas da ke Fatakwal.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan daban sun lalata muhimman kayayyaki a sakatariyar APC da ke Fatakwal, babban brnin jihar Ribas.
Tun ranar Alhamis ƴan Najeriya suka fara zanga-zangar lumana domin nuna damuwarsu kan halin tsadar rayuwa da mutane ke fama da ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan daba sun yi wa jam'iyyar APC ɓarna
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan daban sun mamaye sakatariyar APC da ke titin Fatakwal zuwa Aba, inda suka ɓalla ƙaton allon da ke kofar shiga.
Har ila yau masu zanga zangar sun karya babbar ƙofar shiga da rumfunan da jami'an tsaro ke amfani da su kafin daga bisani a yi nasarar fatattakar su.
Da yake zantawa da manema labarai a Fatakwal, Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC a Jihar Ribas, Cif Tony Okocha, ya yi tir da lamarin.
APC ta gano masu hannu a harin
Okocha ya ce yana zargin cewa wasu manyan mutane ne suka dauki nauyin wannan barnar da aka yiwa APC saboda suna fargabar karɓuwar jam’iyyar a jihar.
A ruwayar Channels tv, shugaban APC ya ce:
"Ana ta maganar cewa ƴan daba sun lalata sakateriyar APC da ke titin Fatakwal zuwa Aba, mun san waɗanda suka ɗauki nauyinsu kuma ba mu tsoron fallasa sunayen su saboda lamarin ya zama siyasa.
"Ko sau miliyan za a kai mana hari ba zai sa mu kame bakinmu ba, dole mu kare al'ummar jihar Ribas. Ba zai hana mu sukar gwamnati mara alƙibla ba, ba abin da zamu fasa."
Kotun ta ƙara taƙaita zanga-zanga
A wani rahoton kuma babbar kotun jihar Legas ta ƙara yanke hukunci kan wuraren da ta amince matasa su yi zanga-zanga.
Mai shari'ar ta tsawaita umarnin cewa ba ta yarda a yi zanga zanga a ko ina ba sai wurare biyu watau Preedom Park da Peace Park.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng