Gwamna Zai Rabawa Matasa Kyautar Biliyoyin Naira Saboda ba Su Shiga Zanga Zanga ba
- Gwamnan jihar Ebonyi ya nuna farin ciki bisa yadda matasa suka masa biyayya, suka ƙi shiga zanga-zangar da aka fara a Najeriya
- Francis Nwifuru ya bayyana cewa gwamnati ta ware N1.3bn domin rabawa matasa 1,300 tallafin da za su kama sana'a su dogara da kansu
- Gwamnan ya ce wannan na ɗaya daga cikin abubuwan zai yi wa matasan Ebonyi domin nuna godiya da biyayyar da suka masa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi Francis Nwifuru ya ce a yunkurinsa na rage radadin da matasa ke ciki da sa su dogaro da kansu, gwamnatinsa za ta tallafawa matasa 1,300.
Gwamna Nwifuru ya ce zai rabawa matasa 1,300 da suka fito daga ƙananan hukumomi 13 na jihar Ebonyi tallafin N1.3bn domin su faɗaɗa kasuwancinsu.
Francis Nwifuru ya fadi haka ne a wurin taron raba tallafi na ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ebonyi/Ohaukwu a garin Akpu Ngbo, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna zai rabawa matasa N1.3bn
Ya ƙara da cewa zai rabawa matasan waɗannan maƙudan kuɗin ne saboda farin cikin biyayyar da suka masa a lokacin da ya nemi su kaucewa zanga-zangar da ake yi.
”Matasan mu sun nuna cewa suna da ɗa'a da biyayya ta hanyar amincewa da rokon da na yi masu na kada su shiga zanga-zangar nan domin amfanin jihar Ebonyi.
"Ba zaku biyo ni bashin rantsuwa ba, na yi maku alƙawarin cewa zan ci gaba da tallafa maku ta yadda za ku riƙa samun damarmaki a rayuwarku.
Ebonyi: Gwamna ya ba da kwangilar titi
Gwamnan ya shaida wa al'umma cewa tuni ya bayar da kwangilar gina titin Umuoguduosha- NigerCem mai tsawon kilomita 24.
A cewarsa, ya ba da aikin ne ga ‘yan kwangila guda biyu domin tabbatar da kammala aikin cikin watanni 18, rahoton The Nation.
Kano: An kama masu hannu a ɗaga tutar Rasha
Kuna da labarin jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS sun cafke masu ɗaukar nauyin telolin tutar ƙasar Rasha a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma.
Tun farko dai jami'an tsaron sun kama telolin da ke ɗinka tutar a ranar Litinin bayan masu zanga-zanga sun fara ɗaga tutocin a kan titi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng