Ana Tsaka da Yin Zanga Zanga, Gwamna a Arewa Ya Tsige Shugaban Hukumar Zabe

Ana Tsaka da Yin Zanga Zanga, Gwamna a Arewa Ya Tsige Shugaban Hukumar Zabe

  • Yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da zanga-zanga, Gwamna Hyacinth Alia ya kori shugaban hukumar zaɓen Benuwai daga aiki
  • Gwamna Alia ya sanar da cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan karɓar shawarwarin majalisar dokokin jihar Benue
  • Tun farko majalisar ta cimma matsaya cewa shugaban BSIEC, Dr. Jonh Chen bai cancanta ba saboda ya gaza cika muradan al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Gwamnan jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya, Hyacinth Alia ya kori shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (BSIEC), Dr John Chen.

Babban sakataren watsa labarai na mai girma gwamnan, Tersoo Kula ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Makurɗi.

Kara karanta wannan

Bayan gwamna a Arewa ya ki albashin N70,000, NLC ta fadi matakin da za ta dauka

Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue.
Gwamna Alia ya kori shugaban hukumar zabe ta jihar Benue Hoto: Fr. Hyacinth Lormen Alia
Asali: Facebook

Ya ce Gwamna Alia ya ɗauki wannan mataki bisa la'akari da shawarwarin majalisar dokokin jihar Benuwai, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Gwamna na tsige shugaban BSIEC

Gwamna Alia ya ƙara da cewa majalisar dokoki ta aiko masa da wasu kudirori da shawarwari domin aiwatarwa wanda matakin sauke shugaban BSIEC na ciki.

A cewarsa, daga cikin shawarwarin da majalisar ta aiko masa har da tsige shugaban hukumar zaɓen jihar Benuwai saboda rashin cancanta ba.

Idan ba ku manta ba a ranar Alhamis ne ƴan majalisar dokokin suka ce shugaban hukumar BSIEC ba ya ɗaukar matakin da ya dace, a koda yaushe yana saɓawa bukatun al'ummar jihar Benue.

Gwamna Alia ya amince da shawarar majalisa

Daily Trust ta ce Gwamna Alia ya amince da shawarin majalisa, inda nan take ya umarci shugaban hukumar zaɓen ya sauka, ya miƙa komai ga sakataren gudanarwa.

Kara karanta wannan

"Muna can muna cin abinci," Shugaban Majalisa ya ta da ƙura kan zanga zanga da ake shirin yi

"Majalisar dokoki ta zargi shugaban BSIEC da rashin sanin ya kamata yayin ɗaukar mataki kuma ya saɓawa mafi rinjayen masu ruwa da tsaki a jihar.
"Haka nan kuma ayyukan da ya yi tun bayan naɗa shi a muƙamin zuwa yanzu sun gaza cimma muradun jama’a. Saboda haka gwamna ya sallame shi daga aiki," in ji sanarwar.

Gwamnatin Borno ta ɗage dokar kulle

A wani labarin kuma gwamnatin Borno ta ɗage dokar hana fita na tsawon awanni uku domin Musulmai su samu damar zuwa masallacin Jumu'a.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Daso Nuhun ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262