Ana Cikin Tsadar Rayuwa, Gwamma Zai Rushe Sabon Gidan Gwamnatin Biliyoyin Naira
- Gwamna Alex Otti ya bayyana shirinsa na rushe sabon gidan gwamnatin jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu ne ya karasa ginin da ya gada kuma ya kaddamar da shi ana gobe zai miƙa mulki a 2023
- Tun bayan rantsar da shi a watan Mayu, Gwamna Otti ya koma garinsu yana tafiyar da harkokin gwamnatin jihar Abia
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya sha alwashin rusa sabon gidan gwamnati da aka gina na biliyoyin Naira a babban birnin Umuahia.
Gwamna Otti ya bayyana hakan ne ranar Asabar a lokacin da yake bude sabon ofishin shugaban karamar hukumar Arochukwu da ke jihar Abia.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ukoha Njoku, ya aikawa jaridar Premium Times ranar Lahadin da ta gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan hawa kan madafun iko, Gwamna Otti ya kauracewa sabon gidan gwamnatin, inda ya koma mahaifarsa yana tafiyar da mulki daga can.
Yadda aka gina gidan gwamnatin Abia
Tsohon gwamnan jihar Okezie Ikpeazu, ne ya kaddamar da sabon gidan gwamnatin ranar 28 ga watan Mayu, 2023 kwana daya kafin sauka daga mulki.
Gwamna Ikpeazu ya gaji aikin daga magabacinsa,Theodore Orji, wanda ya sa harsashin ginin har zuwa matakin rufi.
Babu taƙamaiman kudin da aka kashe amma wata sanarwa da gwamnatin Abia ta fitar a ranar 29 ga Oktoba, 2012 ta nuna cewa ta biya Naira miliyan 175 na yin katanga kaɗai.
Gwamna Otti zai rushe katafaren ginin
A wurin buɗe sabon ofishin ciyaman a Arochukwu ranar Asabar, Gwamna Otti ya ce gwamnatinsa za ta "rushe" sabon gidan gwamnati kafin karshen shekarar nan.
Alex Otti ya ce zai sake gina wani “gidan gwamnati da ya dace a Abia," nan gaba bayan rushe na yanzu, kamar yadda Tribune ta rahoto.
"Ina sanar da ku cewa kafin ƙarshen shekarar nan zamu rusa lalatattun gine-ginen (gidan gwamnatin) kuma zamu yi sabo wanda ya dace da al'ummar jihar Abia."
Gwamna Buni ya rufe makarantun Yobe
A wani rahoton kuma Gwamnatin Yobe ta umarci rufe duka makarantun firamare da sakandire na jihar saboda zanga-zangar da ake shirin yi.
Kwamishinan ilimi a matakin farko, Abba Idriss Adam ne ya sanar da haka a Damaturu, babban birnin jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng