Rai Baƙon Duniya: Majalisar Dattawa Ta Sanar da Mutuwar Fitaccen Sanatan APC

Rai Baƙon Duniya: Majalisar Dattawa Ta Sanar da Mutuwar Fitaccen Sanatan APC

  • Jim kaɗan bayan labari ya fara bazuwa, majalisar dattawa ta fito ta tabbatar da rasuwar sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu, Ifeanyi Ubah
  • Marigayin wanda ɗan jam'iyyar APC ne ya rasu ne yana da shekaru 53 a duniya, wasu majiyoyi sun ce ya je Landan domin a yi masa tiyata
  • Mai magana da yawun majalisar dattawa, Yemi Adaramodu shi ne ya tabbatar da rasuwar yau Asabar, 27 ga watan Yuli, 2024

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da mutuwar sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu, Ifeanyi Ubah.

Mai magana da yawun majalisar, Yemi Adaramodu, shi ne ya tabbatar da rasuwar Sanata Ubah ranar Asabar, 27 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana mai jan hankali bayan mutuwar sanatan APC, ya yi addu'a

Sanata Ifeanyi Ubah.
Majalisar dattawa ta tabbatar da rasuwar Sanata Ifeanyi Ubah Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Sai dai Yemi Adaramodu bai yi cikakken bayanin kan wannan babban rashi da majalisar dattawan ta yi ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa dan majalisar ya tafi kasar Birtaniya ne domin a yi masa tiyata.

Taƙaitaccen bayani game da Ifeanyi Ubah

Sanata Ifeanyi Ubah wanda har zuwa lokacin rasuwarsa dan jam'iyyar APC ne, ya rasu yana da shekaru 53 a duniya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

An fara zaben Ubah a matsayin sanata mai wakiltar Anambra da Kudu a majalisar dattawa a karkashin inuwar jam’iyyar matasa ta YPP a zaɓen 2019.

Ya kuma sake samun nasara a babban zaɓen 2023 duk karkashin inuwar YPP amma daga bisani ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Ƴan bindiga sun taba kai masa hari

Kara karanta wannan

Ifeanyi Ubah: Muhimman abubuwan sani dangane da sanatan APC da ya rasu

A watan Satumban 2022 Ubah ya tsallake rijiya da baya lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai masa hari a hanyarsa ta zuwa Nnewi a Enugwu-Ukwu a jihar Anambra.

Maharan sun buɗewa ayarin motocinsa wuta, inda suka kashe akalla mutane biyar, ciki har da ‘yan sanda biyu.

A lokacin Sanata Ubah ya tsallake rijiya da baya da taimakon motarsa da harsashi ba ya fasawa.

Sojoji 7 sun mutu a Borno

A wani rahoton kuma bom ya tashi da motar sojoji yayin da suke hanyar zuwa kauyen Kukawa da safiyar ranar Alhamis a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa duka sojoji bakwai da ke cikin motar sun mutu sakamakon fashewar bam ɗin a daidai kauyen Bawarti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262