APC Ta Goyi Bayan Tinubu, Ta Fadi Kuskuren da Masu Niyyar Zanga Zanga Ke Yi

APC Ta Goyi Bayan Tinubu, Ta Fadi Kuskuren da Masu Niyyar Zanga Zanga Ke Yi

  • Jam'iyyar APC ta buƙaci masu shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar nan da su sake yin nazari kan buƙatun da suke son gwamnati ta biya musu
  • Sakataren jam'iyyar na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru ya ce ɗaya cikin buƙatun na ganin an watsar da kundin tsarin mulki ba abu ba ne da zai yiwu
  • Ya bayyana cewa da yawa daga buƙatun na su ba su cancanci a yi zanga-zanga a kansu ba saboda abubuwa ne na siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A yayin da ake fargabar shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan, jam’iyyar APC ta buƙaci masu shirya zanga-zangar da su yi watsi da ƙudirinsu.

APC ta buƙaci masu shirya zanga-zangar da su yi watsi da yunƙurinsu na ganin Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da kundin tsarin mulkin shekarar 1999.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu: Minista ya yi magana mai kaushi, ya fadi kulla kullar da ake yi

APC ta goyi bayan Tinubu kan zanga-zanga
APC ta goyi bayan Tinubu kan batun zanga-zanga Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

APC ta goyi bayan Tinubu

Hakan ya fito ne daga bakin sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, bayan kammala taro da shugabannin jam'iyyar na jihohi a Abuja, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ajibola Basiru, ya ce sabon yunƙurin neman shugaban ƙasa ya yi watsi da kundin tsarin mulkin da ya sha alwashin karewa, abu ne wanda ba zai yiwu ba.

A cewar sakataren na jam'iyyar APC, Shugaba Tinubu kaɗai ba shi da ikon yin watsi ko sauya kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ta kowace fuska, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Me APC ta ce kan buƙatun masu zanga-zanga?

Sanata Basiru ya ƙara da cewa taron ya kuma duba buƙatu 15 da masu zanga-zangar suka gabatar, inda suka gano cewa galibin batutuwan da ke ciki ba abubuwan zanga-zanga ba ne.

Ya bayyana cewa da yawa daga cikinsu batutuwan siyasa ne da gyare-gyare ga kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi a Najeriya

"Fadar shugaban ƙasa ita kaɗai ba za ta iya yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima ba. Shugaban ƙasa shi kaɗai ba zai iya daina amfani da kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ba."
"Hakan na buƙatar kaso huɗu bisa biyar na ƴan majalisar tarayya da kaso biyu bisa uku na majalisun dokoki na jihohi. Buƙatarsu ta farko tana neman shugaban ƙasa ya yo abin da ba shi da ikon yi."

- Sanata Ajibola Basiru

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Ƴan majalisa sun ba da shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan majalisar wakilai daga yankin Arewa maso Yamma sun tofa albarkacin bakinsu kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Ƴan majalisar sun buƙaci al’ummar yankin da kada su shiga zanga-zangar wacce aka shirya fara gudanarwa a ranar, 1 ga watan Agustan 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng