Ana Shirin Zanga Zanga, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Ana Shirin Zanga Zanga, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

  • Tsohon ɗan majalisar tarayya daga jihar Legas ya sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
  • Hon Oghene Egoh ya ce tsare-tsaren da Bola Tinubu ya zo da su da nufin ceto Najeriya na daga cikin abubuwan da suka ja hankalinsa zuwa APC
  • Ya ce duk da galibin mutane na tunanin shugaban kasa ya gaza kataɓus amma shi ba haka ya hango lamarin ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Legas - Tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya a mazaɓar Amuwo Odofin, Hon Oghene Egoh, ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a jihar Legas.

Egoh dai ya bar PDP ne da mafi yawan shugabannin jam'iyya na Amuwo Odofin, da dumbin magoya bayansa, duk sun rungumi APC.

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin kamfen PDP ya mayar da zazzafan martani ga Atiku kan zanga zanga

Ganduje da Damagum.
Tsohon ɗan majalisar wakilai, Oghene Egoh ya fice daga PDP zuwa APC Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Umar Damagum
Asali: Facebook

Dalilin Oghene Egoh na shiga APC

Tsohon ɗan majalisar ya ce tsare-tsaren shugaban ƙasa Bola Tinubu da ayyukan alherin Babajide Sanwo-Olu ne suka jawo hankalinsa zuwa APC, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abu na farko da ya jawo hankali na zuwa APC shi ne ajendar shugaban ƙasa Renewed Hope. Na ɗauki wannan mataki na sauya sheka a daidai lokacin da mutane ke ganin Tinubu ya gaza.
"To amma ni na gama karantar tsare-tsarensa kuma ina da kwarin guiwar zai iya gyara Najeriya. Eh tabbas muna cikin wahala amma shugaban ƙasa ya karɓi ƙasar nan a mawuyacin hali.
"Gwammnatin da ta shuɗe ta yi wadaƙa da kuɗin talakawa, Shugaba Tinubu ya zo ya ɗaukar wasu matakai da ake ganin su ne maƙasudin wahalar da ake ciki amma muna fatan za su warkar da Najeriya nan gaba."

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, tsohon kakakin kamfen Atiku ya fice daga PDP zuwa APC

Meyasa ɗan majalisar ya bar PDP?

Egoh ya ƙara da cewa ya yanke shawarar barin PDP ne sakamakon rigimar da ta kaure tsakanin shugabannnin jam'iyyar wanda ya ƙi ci kuma ya ki cinyewa.

A cewarsa, jam'iyyar PDP ta zama gidan rigima musamman a matakin ƙasa kuma a ganinsa ba za ta iya cin zaɓe ba idan har aka ci gaba da tafiya a haka.

Tsohon ɗan majalisar ya ce wannan dalilin ne ya sa ya tattara kayansa ya bar PDP zuwa APC mai mulki, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Ndume ya faɗi dalilin zamansa a APC

A wani rahoton kun ji cewa Muhammad Ali Ndume ya bayyana dalilin da ya sa zai ci gaba da zama a jam'iyyar APC bayan sauke shi daga matsayinsa a majalisa.

Yayin da ya karbi bakunci kungiyoyin mata a Maiduguri, Sanatan Kudancin Borno ya ce zai bi sawun duk inda Gwamna Zulum ya sa ƙafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262