Ministan Tinubu Ya Koma Jam'iyyar APC Yana Halartar Taruka? Gaskiya Ta Bayyana
- APC ta musanta raɗe-raɗin cewa ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike yana taka rawa wajen yanke hukunci a jam'iyyar
- Shugaban APC na rikon kwarya, Cif Tony Okocha ya ce har yanzun Wike ɗan PDP ne kuma ba ya halartar tarukan APC
- Ya ce sun yi iya bakin ƙoƙarinsu domin shawo kansa ya dawo APC amma sun fahimci ba zai taɓa barin jam'iyyar PDP ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Jam'iyyar APC ta reshen jihar Ribas ta musanta raɗe-raɗin cewa ministan Abuja Nyesom Wike yana taka rawa a dukkan matakan da jam'iyyar ke ɗauka.
APC ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa, inda ta bayyana cewa har yanzu tsohon gwamnan bai sauya sheka ya zama cikakken ɗan jam'iyya ba kuma ba ya zuwa taruka.
Mukaddashin shugaban APC na jihar Ribas, Chief Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai a Abuja, kamar yadda Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya koma jam'iyyar APC a Ribas?
Ya ce duk da kokarin da suka yi na shawo kan Wike ya dawo APC sun gane cewa ministan ba zai taɓa barin jam'iyyar PDP ba, Tribune Nigeria ta rahoto.
"Idan na ji irin wannan raɗe-raɗin dariya nake yi, Wike ɗan PDP ne har yanzu, babu alamun zai baro jam'iyyar, mu kuma muna nan a APC.
"Na faɗa maku tun ba yau ba Wike ba ya halartar tarukanmu, mun yi taron masu ruwa da tsaki amma bai zo ba, to taya zai yi tasiri a ayyukan APC ta jihar Ribas?
"Kowa ya san waye Wike, shi minista ne a gwamnatin APC don haka babu gaba a tsakanin mu, amma a ce yana da karfin faɗa aji a cikin mu, to taya? Yana zuwa tarukanmu ne? Amsar ita ce a'a."
- Tony Okocha.
Ɗan majalisan Kogi ya koma APC
A wani rahoton na daban Ɗan majalisar wakilai daga jihar Kogi, Hon. Salman Idris ya sauya sheƙa daga ADC zuwa jam'iyyar APC ranar Talata, 21 ga watan Yuli.
Kakakin majalisar wakilai, Rt Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙar sauya sheƙar da ɗan majalisar ya miƙa masa a zaman yau a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng