Jam'iyyar APC Ta Fara Zawarcin Gwamna a Arewa, Ta Buƙaci Ya Baro PDP
- Jam'iyyar APC ta fara zawarcin Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya
- Masu ruwa da tsakin APC a shiyyar sun fara tuntuɓa da zaman tattaunawa kan yadda za su jawo gwamnan zuwa jam'iyyar APC
- Sun aike da saƙo ga sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru, domin sanar da shi yunƙurinsu na raba Gwamna Mutfwang da PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau - Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a shiyyar Arewa ta tsakiya sun fara tuntuba da zawarcin gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang.
A cewar ƙusoshin jam'iyyar na shiyyar, jawo manyan mutane a jiki masu zuciya irinta Gwamna Mutfwang ya zama dole idan har APC na son sake karɓe jihar Filato.
Hakan na kunshe ne a wata wasiƙa da suka aikawa sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasikar dai na dauke da sa hannun shugaban kungiyar ƴaƴan APC ta Arewa ta tsakiya, Salleh Zazzaga, sannan shugabanta na Nasarawa ya mikawa Bashiru.
Meyasa APC ke shirin jawo Mutfwang?
Wasi sashen wasiƙar ya ce"
"Yana da kyau mu sanar da kai cewa mun fara zawarcin Gwamna Caleb Nutfwang domin ya dawo APC.
"Muna shirin rubuta wasiƙar gayyata a hukumance mu aika masa, jam'iyyar APC reshen jihar Filato da kuma gundumar gwamnan a ƙaramar hukumar Mangu.
"Mun yi shawarwari kuma mun gana da jiga-jigan APC da dama daga Jihar Filato da yankin Arewa ta Tsakiya baki daya don tsara hanyoyin da za mu bi wajen tuntubar gwamnan."
PDP za ta iya rasa jihar Filato
Har ila yau masu ruwa da tsakin APC sun bayyana cewa Gwamna Mutfwang ne kaɗai gwamnan jam'iyyar adawa a shiyyar Arewa ta tsakiya, rahoton Daily Trust.
Don haka a cewarsu, ya kamata a jawo shi ya dawo cikin sauran takwarorinsa wanda hakan ya zama wajibi duba da halin da jam'iyyar APC ta tsinci kanta a shiyyar.
Jam'iyyar PDP ta rasa ƙusoshi zuwa APC
A wani rahoton kuma jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Osun ta rasa wasu manyan kusoshinta waɗanda suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴaƴan PDP da ADP sama da 100 sun fice daga jam'iyyunsu zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng