APC Ta Fusata da Ganin Wani Bidiyo, Ta Buƙaci Majalisa Ta Fara Shirin Tsige Gwamna
- Jam'iyyar APC ta yi tir da kalaman barazana da Gwamna Godwin Obaseki ya yi a wani faifan bidiyo bayan harin filin jirgin sama
- Shugaban APC na jihar Edo, Jarret Tenebe ya yi kira ga majalisar dokoki ta fara shirin tsige gwamnan tun kafin lamari ya dagule
- A bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya, an ji Gwamna Obaseki na gargaɗin cewa idan aka maimaita irin harin 'Najeriya za ta ƙone'
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta mayar da martani kan wani faifan bidiyo da aka ji Gwamna Godwin Obaseki na barazanar cewa 'Najeriya za ta hargitse'.
A faifan bidiyon mai tsawon daƙiƙa 20 da ya bazu, an ji Gwamna Obaseki na PDP yana cewa idan aka maimaita irin harin da ya faru a filin jirgin sama an Benin, 'Najeriya za ta kama da wuta'.
Wane kalamai Gwamna Obaseki ya yi?
A rahoton da Leadership ta wallafa, ta haƙaito Obaseki na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"“Ba zan cika ku da surutu ba, sauran ya rage naku, mun yi shiru ne a ranar Alhamis din da ta gabata, idan suka sake gwada abin da ya faru a ranar, to Nijeriya za ta kone.”
Da yake maida martani kan haka, muƙaddashin shugaban APC na jihar, Jerret Tenebe ya yi tir da kalaman da suka fito daga bakin gwamnan.
Ya kuma roƙi majalisar dokokin jihar Edo ta gaggauta fara shirin tsige Gwamna Obaseki bisa wannan kalamai da ya yi na barazanar ƙone Najeriya, rahoton PM News.
APC ta roki a sauke Gwamna Obaseki
A wata sanarwa da ya fitar, shugaban APC na jihar ya ce:
"Wannan barazana da Obaseki ya yi ga Najeriya da mutanen cikinta ta wuce tunanin mai hankali kuma ya kamata a shawo kan lamarin don gujewa tada zaune tsaye da karya doka da oda a Edo da Najeriya gaba ɗaya."
"Mutanen Edo ba za su zuba ido suna kallon irin siyasar tashin hankalin da gwamna ke jagoranta ba wanda ya ƙara kawo taɓarɓarewar tsaro a jihar.
“Domin daƙile wannan mummunan shiri, muna rokon kakakin majalisar jiha da sauran ƴan majalisa su fara shirin sauke gwamna daga kan mulki."
Shaibu ya zargi Gwamna da kai masa hari
A wani rahoton kuma Kwamared Philip Shaibu ya zargi Gwamna Godwin Obaseki da yunƙurin hallaka shi a hanyar dawowarsa jihar Edo ranar Alhamis.
Mataimakin gwamnan wanda kotu ta mayar kan muƙaminsa ya shigar da ƙara yana neman gwamnan da hadimansa su biya diyyar N5bn.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng