Jam'iyyar APC Ta Fara Zawarcin Mataimakin Gwamnan PDP, Za Ta Kafa Tuta a Ofishinsa
- Jam'iyyar APC ta fara zawarcin mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu bayan harin da aka kai masa a filin jirgin sama
- Shugaban APC na jihar Edo, Jarret Tenebe ya ziyarci Shaibu kuma ya buƙaci ya jefar da PDP saboda yunƙurin ɗaukar ransa
- Kwamared Shaibu ya yabawa Tenebe bisa yadda yake ƙara masa kwarin guiwa, inda ya ƙara jaddada goyon bayansa ga APC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ci gaba zawarcin mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu bayan kotu ta maida shi kan muƙaminsa.
Shugaban APC reshen jihar Edo, Jarrett Tenebe ya yi kira ga Kwamared Shaibu ya jefar da ƙwallon mangwaro ko ya huta da ƙuda kana ya dawo cikin APC.
Tawagar APC ta ziyarci Shaibu
Mista Jarrett Tenebe ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci Shaibu a gidansa da ke Benin, babban birnin jihar Edo ranar Jumu'a, Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tenebe, wanda ya samu rakiyar wasu kusoshin APC, ya bayyana harin da aka kaiwa Shaibu a filin jirgin sama a matsayin wani yunƙuri na ɗaukar rayuwarsa.
"Abin da (ake zargin) jam'iyyar ka ta shirya shi ne ta ɗauki rayuwarka. A halin da muke ciki yanzu kai ne sahihin mataimakin gwamna a jihar Edo.
"Na kawo maka saƙon APC kuma daga yanzu tutarmu za ta fara kaɗawa a ofishinka,” in ji Tenebe.
Philip Shaibu ya yabawa shugaban APC
A nasa jawabin, Philip Shaibu ya yabawa shugaban APC kan yadda a koda yaushe yake kara masa kwarin gwiwa tun lokacin da ya tsinci kansa a rigima a jam’iyyar PDP.
A cewarsa, wannan matakin kulawa shine abin da ake bukata a kowane irin shugabanci, kamar yadda Daily Nigerian ta kawo.
"Shugaban jam’iyyar PDP bai taba ɗaga waya ya kirani ko ya yi kokarin warware rikicin da ke faruwa ba duk da na nuna cewa ni dan jam’iyya ne.
"Da yardar Allah Sanata Monday Okpebholo da Dennis Idahosa na jam'iyyar APC ne za su zama gwamna da mataimakinsa a jihar Edo," in ji Shaibu.
Shaibu ya caccaki Gwamna Obaseki
A wani rahoton kuma Kwamared Philip Shaibu ya zargi Gwamna Godwin Obaseki da yunƙurin hallaka shi a hanyar dawowarsa jihar Edo ranar Alhamis.
Mataimakin gwamnan wanda kotu ta mayar kan muƙaminsa ya shigar da ƙara yana neman gwamnan da hadimansa su biya diyyar N5bn.
Asali: Legit.ng