Sanata Ndume Ya Maida Martani Ga Ganduje, Ya Faɗi Yadda Buhari da Tinubu Suka Jawo Shi APC
- Sanata Ali Ndume ya mayar da martani ga shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Ganduje kan shawarar barin jam'iyya mai mulki
- Ndume ya bayyana yadda Muhammadu Buhari da shugaban ƙasa Bola Tinubu suka ba shi umarnin ya dawo APC a wancan lokacin
- A ranar Laraba da ta gabata majalisar dattawa ta tsige Ndume daga matsayin mai tsawatarwa bayan APC ta aika wasiƙa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno - Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Tinubu ne suka haɗu suka jawo shi zuwa APC tun farko.
Sanata Ndume ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa shafinsa na Facebook ranar Jumu'a.
Idan ba ku manta ba a ranar Laraba aka sauke shi daga mukamin mai tsawatarwa a majalisar dattawa biyo bayan wasiƙar da shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya aika.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wasiƙar jam'iyyar APC ta buƙaci a sauke Sanata Ndume daga matsayinsa kuma ta ba shi shawarin ya tattara kayansa ya koma jam'iyyar adawa.
Ali Ndume ya mayar da martani ga Ganduje
Da yake mayar da martani, Ali Ndume ya ce yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa APC kuma ya zama cikakken mamban jam'iyyar gabanin Ganduje ya shiga.
Sanatan ya ce a wancan lokacin, Buhari da Tinubu ne suka umarce shi ya sa hannu a wata takarda da ke nuna zai koma APC a masaukin gwamnan Imo da ke Abuja.
"Ni uban jam'iyya ne, na shiga APC tun kafin Ganduje ya shigo saboda ina ɗaya daga cikin ƴaƴan PDP da suka taho aka kafa APC, kuma ba bisa ra'ayina na yi hakan ba sai da na tattauna da mutanen mazaɓa ta.
"Ina cikin sanatoci 22 da suka bada haɗin kai wajen kafa APC, ana kiran mu nPDP a wancan lokacin, tarihi baya ƙarya idan kuka duba sunana ne na 21. Da farko ban so shiga APC ba.
"Amma Buhari da shugaban ƙasar mu na yanzu Tinubu suka kira ni suka umarci na dawo APC a masaukin gwamnan jihar Imo."
- Muhammad Ali Ndume.
Duk da haka Sanata Ndume, mai wakiltar Kudancin Borno a majalisar dattawa ya ce zai tuntuɓi mutanen mazaɓarsa kuma idan har suka amince babu makawa zai bar APC.
Kalaman da suka jefa Ndume a matsala
A wani rahoton kun ji cewa Muhammad Ali Ndume ya gamu da fushin abokan aikinsa a majalisa saboda wasu kalamai da ya yi a fili kwanaki.
Sanatan na Kudancin jihar Borno ya ba da labarin yadda ya tunkari gwamnati kan halin kuncin da talakawa su ke ciki.
Asali: Legit.ng