Mataimakin Gwamna Ya Tsokano Rigima, Ya Faɗi Gwamnan PDP da Ya Yi Yunƙurin Kashe Shi

Mataimakin Gwamna Ya Tsokano Rigima, Ya Faɗi Gwamnan PDP da Ya Yi Yunƙurin Kashe Shi

  • Kwamared Philip Shaibu ya zargi Gwamna Godwin Obaseki da yunƙurin hallaka shi a hanyar dawowarsa jihar Edo ranar Alhamis
  • Mataimakin gwamnan wanda kotu ta mayar kan muƙaminsa ya shigar da ƙara yana neman gwamnan da hadimansa su biya diyyar N5bn
  • Shaibu ya kuma yi iƙirarin cewa tun da ya ayyana neman takarar gwamna, Obaseki ya lashi takobin ganin bayansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo da aka mayar, Philip Shaibu ya yi ikirarin cewa harin da aka kai masa ranar Alhamis wani yunkuri ne na ganin bayansa.

Shaibu ya kuma yi zargin cewa Gwamna Godwin Obaseki ne ya shirya kai harin da nufin raba shi da duniya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari, sun kashe basarake mai martaba da ɗansa a Arewa

Shaibu da Gwamna Obaseki.
Philip Shaibu ya zargi Gwamna Obaseki da hannu a kai masa harin da nufin hallaka shi Hoto: Comrade Shaibu, Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani ga ikirarin gwamnatin jihar na cewa shi ne ya shirya harin wanda ya zama ajalin insufekta Akor Onuh.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin gwamnan ya shaidawa ƴan jarida cewa ya yi mamakin harin da aka kai masa wanda ya ɗora alhakin a kan gwamna, Punch ta ruwaito.

Kwamared Shaibu ya ƙara da cewa a bara ya yi ƙoƙarin hana duk wata zanga-zangar goyon bayansa domin kaucewa arangama da ƴan daban gwamnatin jihar.

Shaibu ya maka Obaseki a kotu

Ya ce tuni ya maka gwamna, kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Chris Nehikhare, da hadimin gwamna na ɓangaren midiya, Crusoe Osagie a kotu kan zargin ɓata masa suna.

Philip Shaibu ya ce bai yi mamakin yadda Nehikhare da Osagie ke nanata cewa an tsige shi daga mukamin mataimakin gwamnan Edo ba, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fara zawarcin mataimakin gwamnan PDP, za ta kafa tuta a ofishinsa

A cewarsa, ba su nazari kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke ba gabannin su yi masa martani.

Edo: Mataimakin gwamna ya zargo Obaseki

"Bari na faɗa maku harin da aka kai mun ranar Alhamis da ta shige wani shiri ne na gwamna da nufin hallaka ni.
"Gwamnan ya sha alwashin halaka ni a lokacin da na kafe kan baka ta wajen neman kujerar gwamna. Sun ce ni na kitsa harin amma na iso Benin lafiya daga Abuja.
"Taya ƴan daba suka yi mun kwantan ɓauna? Dama sun san zan shigo garin ne? Na riga na shigar da karar gwamna, Nehikhare da Osagie tare da neman diyyar N5bn saboda ɓata mun suna."

- Philip Shaibu.

Edo: Shaibu ya naɗa hadimai a ofishinsa

A wani rahoton kun ji cewa Mataimakin gwamnan jihar Edo da kotu ta dawo da shi kan mulki ya naɗa sababbin hadimai a ofishinsa ranar Jumu'a

Kwamared Philip Shaibu ya naɗa shugaban ma'aikata, sakataren watsa labarai da manyan masu taimaka masa na musamman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262