Sukar Tinubu: Sanata Ndume Ya Mayar da Martani Kan Sauke Shi a Muƙamin Majalisa
- Ali Ndume ya mayar da martani bayan majalisar dattawa ta sauke shi daga muƙamin mai tsawatarwa kwanaki biyu da suka wuce
- Sanatan na Borno ya kuma yi watsi da muƙamin da aka naɗa shi na shugaban kwamitin kula da harkokin yawon buɗe ido
- Ndume ya ce yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar APC don haka batun ya sauya jam'iyya ma ba ta taso ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - A karon farko, Sanata Muhammed Ali Ndume ya mayar da martani bayan sauke shi daga muƙamin mai tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya.
Bayan sake sauraron hirar da ta sa aka ɗauki matakin tsige shi, Ali Ndume ya ce kalaman da ya yi ba su kai girman da jam'iyyar APC za ta sauya shi a majalisa ba.
Sanata Ali Ndume ya yi magana
Kamar yadda Channels tv ta tattaro, majalisar dattawa ta sauke Ndume daga matsayin mai tsawatarwa ne bayan ya soki salon gwamnatin Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ali Ndume ya yi martani ne a gidansa da ke Maiduguri ranar Jumu'a, 19 ga watan Yuli, kwanaki biyu bayan APC ta sauke shi daga muƙaminsa a majalisa.
Ndume ya ƙara da cewa bai taɓa sha'awar zama mai tsawatarwa ba bayan ya yi aiki a matsayin jagoran majalisar dattawa ta 8, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ɗan majalisar ya ce bayan ya jagoranci kamfen da ya bai wa Godswill Akpabio nasarar zama shugaban majalisar dattawa, an ba shi damar ya zaɓi kwamitin da yake so.
Ndume zai fice daga jam'iyyar APC?
Dangane da batun shawarin da aka ba shi na ya bar APC, Ali Ndume ya ce shi uban jam'iyya ne domin yana cikin waɗanda suka kafa APC.
A cewarsa, yana ɗaya daga cikin sanatoci 22 da suka baro PDP domin kafa APC a lokacin shugaban jam'iyya na yanzu, Abdullahi Ganduje yana mataimakin gwamnan Kano.
Tinubu zai miƙa kudirin albashi ga majalisa
A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tura kudirin sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 zuwa majalisar tarayya a makon gobe.
Mai bai shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka bayan cimma matsaya da ƴan kwadago.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng