Ganduje Ya Buƙaci Sanata Ya Fice Daga APC Mai Mulki Ya Koma Jam'iyyar Adawa
- Jam'iyyar APC ta shawarci sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Muhammed Ali Ndume ya sauya sheka zuwa wata jam'iyyar adawa
- Hakan ya biyo bayan sauke Ndume daga matsayin mai tsawatarwa a majalisar dattawa sakamakon sukar da ya yiwa Bola Tinubu
- Tun farko Sanata Ndume ya soki gwamnatin Bola Tinubu inda ya yi iƙirarin cewa an rufe duk wata ƙofa ta ganin shugaban ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta sauke Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu daga matsayin babban mai tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya.
Hakan na kunshe ne a wata takardar da jam'iyyar APC ta aika majalisar dattawan mai ɗauke da sa hannun shugaban jam'iyya, Abdullahi Ganduje da sakatare.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta takardar a zaman sanatoci na yau Laraba, 17 ga watan Yuli, 2024, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta buƙaci Ndume ya sauya sheƙa
A cikin takardar, APC ta bukaci Sanata Ndume ya tattara kayansa ya bar jam'iyya mai mulki, ya koma jam'iyyar da ya ga dama, Daily Trust ta kawo labarin.
Bugu da ƙari, jam'iyyar APC ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan caccakar da Ndume ya yi wa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Idan ba ku manta ba a wata hira da ya yi kwanan nan, Muhammed Ali Ndume ya soki gwamnatin Tinubu, inda ya yi ikirarin cewa hadimai sun babbake komai.
Silar fadan Sanata Ndume da APC
Sanata Ali Ndume ya kuma koka kan cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta rufe dukkan kofofin da za a rika fada mata gaskiya kan halin da ake ciki.
Wannan kalamai ba su yi wa APC da wasu sanatoci daɗi ba, wanda hakan ya sa jam'iyyar ta sauke shi daga matsayin mai ladabtarwa a majalisa.
APC ta kuma ɓa shi shawarar cewa zai iya ficewa daga APC ya koma wata jam'iyya daga cikin jam'iyyun adawa.
Majalisa ta gano yadda ake asarar $9bn
A wani rahoton kuma Majalisar wakilai ta bayyana takaici kan yadda kasar nan ke tafka asara kan hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.
Shugaban kwamitin ma'adanai, Hon. Jonathan Gbefwi ya ce ana asarar akalla $9bn duk shekara, wanda hakan ba karamar asara ba ce
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng