Majalisar Dattawa Ta Tsige Sanatan APC Daga Mukaminsa, Ta Maye Gurbinsa Nan Take

Majalisar Dattawa Ta Tsige Sanatan APC Daga Mukaminsa, Ta Maye Gurbinsa Nan Take

  • Majalisar dattawan Najeriya ta sauke Sanata Mohammed Ali Ndume daga kujerar babban mai tsawatarwa na jam'iyya mai mulki
  • Sanatocin jam'iyyar ne suka kaɗa kuri'ar tsige Sanata Ndume kuma suka maye gurbinsa da Sanata Tahir Mungono mai wakiltar Borno ta Arewa
  • A wata wasiƙa da jam'iyyar APC ta aika majalisar, ta shawarci Ali Ndume ya tattara kayansa ya sauya sheƙa zuwa wata jam'iyyar ta daban

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar dattawa, a ranar Laraba, ta sanar da tsige Sanata Mohamed Ali Ndume (APC, Borno ta Kudu) daga matsayin babban mai tsawatarwa.

Hakan ta faru ne a lokacin da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya buƙaci saanatocin jam'iyyar APC su kaɗa kuri'ar murya kan tsige Ndume.

Kara karanta wannan

Ganduje ya buƙaci Sanata ya fice daga APC mai mulki ya koma jam'iyyar adawa

Sanata Akpabio, Ali Ndume da Abdullahi Ganduje.
Majalisar dattawa ta sauya babban mai tsawatarwa bayan tsige Sanata Ali Ndume Hoto: @Imranmuhdz, @SPNigeria, @OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Majalisar dattawa ta maye gurbin Ndume

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Sanatocin jam'iyya mai mulki sun kaɗa kuri'ar amincewa da tsige Sanata Ndume daga matsayin mai ladabtarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu Sanata Tahir Mungono mai wakiltar Borno ta Arewa a inuwar jam'iyyar APC ya maye gurbin Ndume, kamar yadda Channels tv ta tattaro.

Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kalilan bayan Sanata Ndume ya fito ya soki gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

APC ta aika wasika zuwa majalisar dattawa

Har ila yau a wata wasiƙa da jam'iyyar APC mai mulki ta aika majalisar dattawa, ta buƙaci Sanata Ali Ndume ya fice daga jam'iyyar ya koma duk jam'iyyar da ta kwanta masa a rai.

Wasiƙar dai na ɗauke da sa hannun shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da sakatare Barista Ajibola Bashiru.

Kara karanta wannan

Ondo: Dan takarar gwamna ya fadi mafi karancin albashin da zai biya idan ya ci zabe

Sanatoci na kokarin dakatar da Ndume

Rahotanni daga majalisar sun nuna cewa wasu sanatocin da ke goyon bayan Tinubu sun yi yunƙurin ganin an dakatar da Ali Ndume kamar yadda aka yiwa Abdul Ningi.

Wasu sanatoci uku da su ka fito daga Kudu maso Yamma a jihohin Ekiti, Ogun da Legas sai karin guda daga Kogi ne ke kokarin rura wutar dakatar da Sanatan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262