Masoyan Tinubu Za Su Dauki Mataki kan Sanata Ali Ndume kan Sukar Shugaban Kasa

Masoyan Tinubu Za Su Dauki Mataki kan Sanata Ali Ndume kan Sukar Shugaban Kasa

  • An bankado shirin wasu 'yan majalisa daga Kudancin kasar nan na dakatar da Sanata Ali Ndume kamar yadda aka yiwa Abdul Ningi
  • Wannan ya biyo bayan rashin jin dadin yadda Sanatan ya caccaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan salon mulkinsa
  • An gano 'yan majalisar sun fito daga jihohin Ekiti, Ogun, Legas da Kogi, inda su ke shirin tsige Sanata Ndume daga mukaminsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kalaman Sanata Ali Ndume kan Bola Tinubu bai yi wa 'yan majalisa masu goyon bayan shugaban dadi ba. Yanzu haka an bankado kokarin wasu daga cikin 'yan majalisar na kitsa yadda za a dakatar da Sanata Ndume kamar yadda aka yiwa Abdul Ningi kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Abdullahi Ganduje ya fadi dalilin karuwar cin hanci da rashawa

Sen. Muhammad Ali Ndume
Wasu 'yan majalisar Kudancin kasar nan na yunkurin dakatar da Sanata Ali Ndume Hoto: Sen. Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa daga cikin matakin da wasu 'yan majalisa ke son dauka har da tsige shi daga mukamin bulaliyar majalisa.

Wasu sanatoci uku da su ka fito daga Kudu maso Yamma a jihohin Ekiti, Ogun da Legas sai karin guda daga Kogi ne ke kokarin rura wutar dakatar da Sanatan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene laifin Sanata Ndume?

Arise TV ta wallafa cewa laifin Sanata Ali Ndume shi ne sukar shugabancin kasar nan, inda ya ce Shugaba Tinubu bai san halin da ake ciki ba.

Ana ganin kamar bai kamata a ce bulaliyar majalisa ya caccaki salon mulkin Tinubu a bainar jama'a ba.

Haka kuma 'yan majalisar ba su ji dadin yadda Sanata Ndume ya yi ikirarin cewa wasu sun hana shugaban sanin matsalolin 'yan kasa.

Shugaban majalisa ya shiga tsaka mai wuya

Kara karanta wannan

"A yi hakuri," Sarki ya roki 'yan Najeriya su ba gwamnatin Tinubu lokaci

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya shiga tsaka mai wuya kan kokarin dakatar da Sanata Ali Ndume.

Sanatan na gaba gaba wajen yakin neman zaben da ya tabbatar da Akpabio a Kujerarsa ta shugaba a majalisar.

Sai dai zuwa yanzu majalisa ba ta tabbatar da zargin daukar mataki a kan sanatan ba.

Tibubu: APC ta caccaki Sanata Ndume

A baya mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta ce bai kamata Sanata Ali Ndume ya furta kalamansa kan shugaba Tinubu ba.

Jami'in hulda da jama'a na jam'iyyar, Felix Morka ya zargi Sanata Ndume da nuna shugaban kasar ya gaza sauke nauyin 'yan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.