Magana Ta Kare, Gwamna Abba Kabir Ya Ƙirƙiro Sababbin Masarautu 3 a Jihar Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da ƙirƙiro sababbin masarautu uku masu daraja ta biyu a jihar Kano
- Wannan na zuwa ne bayan majalisar dokokin Kano ta amince da kudirin kafa masarautun Gaya Rano da Ƙaraye a zaman yau Talata
- Kudirin dai ya bai wa gwamna cikakken ikon naɗa waɗanda suka cancanta a matsayin sarakunan waɗannan masarautu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaɓa hannu kan kudurin dokar kirkiro sababbin masarautun guda uku a fadar gwamnatinsa da ke cikin birnin Kano ranar Talata.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.
Tun farko majalisar dokokin Kano ta amince da dokar kafa masarautu 2024 bayan kudirin ya tsallake karatu na uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda kudirin ya raba sababbin masarautu
Kudirin ya kunshi barin masarautar Kano a matsayin mai daraja ta farko da kuma ƙirƙiro sababbin masarautu uku Rano, Gaya da Karaye a matsayin masu daraja ta biyu.
Masarautar Rano ta kunshi kananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya yayin da Masarautar Gaya tana da kananan hukumomin Gaya, Albasu da Ajingi.
Sai kuma masarautar Karaye wanda ƴan majalisar suka amince kananan hukumomin Karaye da Rogo su kasance a karƙashinta.
Har ila yau, sashe na 7 na dokar ya baiwa gwamnan ikon nada duk wanda ya dace a matsayin sarki mai daraja ta biyu bisa tanadin sashe na 4 na kudirin.
Gwamna Abba zai naɗa sarakuna 3
Da yake jawabi bayan rattaba hannu kan dokar, Gwamna Abba ya ce nan ba da jimawa ba zai sanar da sunayen sababbin sarakunan masarautun.
"Ina taya sabbin masarautu murna, kuma ina kira gare su da su maida hankali wajen yi wa al'umma hidima. Nan bada daɗewa ba gwamnati za ta naɗa sababbin sarakuna," in ji shi.
Gwamnatin Kano ta yaba da hukuncin kotu
A wani rahoton kun ji cewa Gwamnatin Kano ta ce ba ta yi mamakin hukuncin kotu da ya tabbatar da nadin Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II ba.
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka yayin martani kan hukuncin babbar kotun jiha.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng