Jam'iyyar APC Ta Ba Gwamnan PDP Shawara Kan 'Yancin Kananan Hukumomi

Jam'iyyar APC Ta Ba Gwamnan PDP Shawara Kan 'Yancin Kananan Hukumomi

  • Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Rivers ta buƙaci gwamnan jihar da ya mutunta hukuncin da Kotun Ƙoli ta yi kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi
  • APC ta buƙaci Gwamna Siminalayi Fubara da ya rushe shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi da ya naɗa
  • Hakan na zuwa ne bayan Kotun Ƙoli ta yi hukuncin cewa shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi sun saɓawa doka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Jam’iyyar adawa ta APC a jihar Rivers, ta yi kira ga Gwamna Siminalayi Fubara da ya mutunta hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Ta buƙace shi da ya rushe shugabannin riƙo da ya naɗa a ƙananan hukumomin saboda hakan ya saɓa doka biyo bayan hukuncin kotun.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa 'yancin cin gashin kan kananan hukumomi ba zai yi aiki ba" Inji Tsohon gwama

Jam'iyyar APC ta shawarci Gwamna Siminalayi Fubara
Jam'iyyar APC ta bukaci Gwamna Fubara ya rushe shugabannin riko na kananan hukumomi Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Wace shawara APC ta ba Gwamna Fubara?

Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar APC a jihar, Chibuike Ikenga, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ya yi da jaridar The Punch a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chibuike Ikenga ya yi kira ga Gwamna Fubara da ya rushe shugabannin riƙon da ya naɗa domin yin biyayya ga hukuncin na Kotun Ƙoli.

"Kotun Ƙoli ita ce ta ƙarshe. Matsayarsu ita ce shugabannin riƙo haramtattu ne kuma sun saɓawa kundin tsarin mulki, domin haka mu ma a kan wannan matsayar mu ke."
"Dole ne mu yi biyayya, dole ne mu bi hukuncin Kotun Ƙolin wacce ita ce ta ƙarshe ta yanke."
"Muna sane musamman a jihar Rivers cewa Gwamna Fubara ba ya bin doka, ba ya bin umarnin hukuncin kotu, haka kuma ba ya bin ƙa’idojin da tsarin mulki ya tanada, domin haka ba za mu yi mamaki ba."

Kara karanta wannan

Daga karshe Gwamna Zulum ya fadi dalilin kai harin kunar bakin wake a Borno

- Chibuike Ikenga

Chibuike Ikenga ya ce tun da dadewa gwamnoni suna ƙwace ikon ƙananan hukumomi tare da hana su samun kuɗaɗen da ya kamata su samu.

Batun kawo ƙarshen rikicin Wike-Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan rikicin siyasar da ke tsakanin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike.

Shehu Sani ya bayyana cewa Allah ne kaɗai zai iya magance rikicin siyasar da ke tsakanin mutanen biyu waɗanda ba sa ga maciji da juna a halin yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng