Ganduje Ya Cika da Murna Bayan Ya Yiwa PDP Wata Babbar Illa
- Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Alhaji Umar Abdullahi Ganduje ya bayyana farin cikinsa kan shigowar Sanata Anyim Pius Anyim zuwa jam'iyyar
- Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana shigowar tsohon shugaban na majalisar dattawa a matsayin babban alheri
- Ya bayyana cewa za anba shi dama kamar sauran tsofaffin ƴaƴan jam'iyyar domin ya zo ya bayar da irin ta sa gudunmawar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shigowar tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Pius Anyim zuwa jam’iyyar a matsayin "babban alheri".
Ganduje ya nuna murnarsa ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Mista Edwin Olofu, ya fitar.
Me Ganduje ya ce kan dawowar Anyim zuwa APC
Sanarwar wacce aka fitar a ranar Lahadi a Abuja, ta ruwaito Ganduje na faɗin cewa, ƙwarewar Sanata Anyim za ta yi amfani ga jam'iyyar APC, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da farko Ganduje ya karɓi Sanata Anyim wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC yayin wani taron yaƙin neman zaɓe a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi.
"Na yi farin cikin tarbar wannan muhimmin mutumin zuwa cikin jam'iyyar mu."
"Ina son na ba ka tabbaci a madadin shugaban ƙasa Bola Tinubu, cewa muna maka maraba da zuwa babbar jam'iyyar siyasa a nahiyar Afirika."
"Ina ba ka tabbacin cewa za a ba ka dama kamar yadda aka ba tsofaffin mambobin jam'iyyar mu ta yadda za ka ba da taka irin gudunmawar."
- Abdullahi Umar Ganduje
Jaridar Vanguard ta ce shugaban na jam'iyyar APC ya kuma buƙaci yankin Kudu maso Gabashin Najeriya da bar jam'iyyar adawa ya shigo a dama da shi a jam'iyya mai mulki.
APC ta caccaki Sanata Ali Ndume
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta caccaki Sanata Ali Ndume bisa kalaman da ya yi kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
APC ta bayyana cewa kalaman Ndume na cewa ba a ganin shugaban ƙasan kuma bai san halin da ake ciki a ƙasar nan ba, ba su dace ba.
Asali: Legit.ng