Babban Jigo Kuma Tsohon Kakakin Kamfen Atiku Abubakar Ya Sauya Sheƙa Daga PDP

Babban Jigo Kuma Tsohon Kakakin Kamfen Atiku Abubakar Ya Sauya Sheƙa Daga PDP

  • Babban jigo kuma tsohon kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ya fice daga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP
  • Daniel Bwala ya bayyana cewa ya tattara kayansa ya fice daga PDP kuma ya kusa komawa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
  • Sai dai ana ganin wannan ba wani abin mamaki ba ne idan aka yi la'akari da yadda Bwala ya koma kare Bola Tinubu bayan kammala zaɓen 2023

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Daniel Bwala, lauya kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa a ƙasar nan ya bayyana cewa ya jima da barin babbar jam'iyyar adawa PDP. 

Mista Bwala ya ce bayan barin PDP, a yanzu yana dab da sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sabuwar tafiya: Hotunan yadda Kwankwaso ya kaddamar da sabon tambarin NNPP a Abuja

Daniel Bwala da Bola Tinubu.
Bwala ya tabbatar da cewa ya bar PDP kuma yana hanyar shiga APC Hoto: Daniel Bwala
Asali: Twitter

Channels tv ta tattaro cewa Bwala ya kasance kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a cikin shirin siyasa a yau na kafar talabajin na Channels ranar Alhamis, Mista Bwala ya ce shi ba ɗan PDP ba ne saboda ya fice daga cikinta.

"Eh na riga na bar babbar jam'iyyar adawa, a yanzu na raba gari da jam'iyyar PDP," in ji shi.

Wace jam'iyya Bwala zai koma?

Yayin da aka tambaye shi ko yanzu ya koma jam’iyyar APC ne, sai ya ce, “Ina kusa” da sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki bayan baro PDP.

Sauya sheƙar da tsohon babban jigon PDP ba zai zama abin mamaki ba ga masu bibiyar al'amuran siyasa duba da yadda yake ɗasawa da Gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya faɗi jihar da za ta fara amfani da sabon tambarin NNPP a Najeriya

Bwala wanda ya kasance mai sukar Bola Tinubu a gabanin zaben 2023, ya zama daya daga cikin masu kare manufofin shugaban kasa bayan zaben.

A watan Janairu, ya kai wa Bola Tinubu ziyara har fadar shugaban kasa da ke Abuja inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su marawa gwamnati mai ci baya.

Sai dai a halin yanzun, tsohon kakakin kamfen Atiku ya tabbatar da cewa ya bar PDP kuma yana dab da shiga APC.

Kano: Masud Doguwa ya koma PDP

A wani rahoton kun ji cewa yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan sarautar Kano, jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta ranar Jumu'a.

Sanata Masud Doguwa ya jagoranci ɗumbin magoya bayansa daga APC sun koma PDP, ya ce gwamnatin Tinubu ba ta da alƙibla.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262