APC Ta Wargaje Kashi 3 a Zamfara, Jigon Jam’iyya Ya Kafa Sabuwar Sakateriya

APC Ta Wargaje Kashi 3 a Zamfara, Jigon Jam’iyya Ya Kafa Sabuwar Sakateriya

  • Rikicin jam'iyyar APC ya kara ƙamari a jihar Zamfara yayin da aka kara samun tsagin da ya ɓalle daga uwar jam'iyyar
  • Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kaura Namoda da Birnin Magaji ya ware shi da mutanensa saboda wasu dalilai
  • A yanzu haka jam'iyyar APC ta rabu gida uku a Zamfara inda kowane tsagi ke ikirarin riko da jagorancin jami'yyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Jami'yyar APC mai mulki ta kara shiga ruɗani a Zamfara bayan dan majalisar tarayya ya kafa tsaginsa.

A kwanakin baya ne dai Sanata Kabiru Garba Marafa ya kafa tsagin jami'yyar shi da magoya bayansa.

Jihar Zamfara
APC ta shiga rudani a Zamfara. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa dan majlisar tarayyar da ya ɓalle daga jami'yyar ya kafa sabuwar sakateriya.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya fara samun koma baya, shugabannin NNPP sun koma APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zamfara: Sani Jaji ya kafa tsagin APC

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kaura Namoda da Birnin Magaji, Sani Jaji ya kafa tsagin jami'yyar APC a Zamfara.

Shugaban sabon tsagin, Aminu Abubakar, ya ce matakin da suka dauka ya zama dole ne saboda rashin kyautata musu da aka yi a jami'yyar.

Zamfara: Dalilin kafa sabon tsagin APC

Shugaban sabon tsagin, Aminu Abubakar ya bayyana cewa yin watsi da bangaren Sani Jaji ne yasa suka ware nasu bangaren.

Aminu Abubakar ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki a jami'yyar sun yi taro a Kaduna amma aka ware Sani Jaji ba tare da gayyata ba.

Ya kara da cewa a yanzu haka sun nada shugabannin rikon kwarya kuma nan gaba kadan za su gudanar da zabe, rahoton Vanguard.

A yanzu haka dai a jihar Zamfara akwai jami'yyar APC ƙarƙashin Bello Matawalle/Abdulaziz Yari, Sanata Kabiru Marafa da Sani Jaji.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan mutuwar mahaifiyar Minista, Tinubu ya nuna alhini

Zamfara: APC ta yi magana kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake fama da matsalar tsaro a Zamfara, jam'iyyar APC ta bayyana Gwamna Dauda Lawal a matsayin mai laifi.

Jam'iyyar ta ce duka abin da ke faruwa laifin Dauda Lawal ne saboda yaki hada kai da Bello Matawalle domin kawo karshen matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng