Badakalar N423bn: Dan Majalisa Ya Yiwa El Rufai Wankin Babban Bargo

Badakalar N423bn: Dan Majalisa Ya Yiwa El Rufai Wankin Babban Bargo

  • Ɗan majalisa mai wakiltar Zaria a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya yi martani kan matakin da Nasir El-Rufai ya ɗauka na zuwa kotu kan binciken da ake yi masa
  • Mahmud Lawal ya bayyana matakin a matsayin dariya inda ya nuna kaɗuwa kan yadda El-Rufai yanzu yake son a mutunta bayan ya daɗe yana watsi da ita
  • Ya koka da cewa a lokacin mulkin tsohon gwamnan, an karkatar da dukiyar jihar da sunan za a gudanar da ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - An bayyana matakin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ɗauka na shigar da ƙara kan zargin karkatar da naira biliyan 432 a matsayin abin dariya.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga 100 sun kai hari kan bayin Allah, sun tafka mummunar ɓarna

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Zaria a majalisar dokokin jihar Kaduna, Mahmud Lawal, ya bayyana haka.

Dan majalisa ya caccaki El-Rufai
Dan majalisa ya caccaki El-Rufai kan kai kara kotu Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

Mahmud Lawal ya bayyana hakan ne dai a zantawarsa da manema labarai a Kaduna, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan majalisa ya caccaki El-Rufai

Ɗan majalisar ya bayyana rashin jin daɗinsa kan abin da ya bayyana da cewa yadda El-Rufai ya koma yana son a mutunta doka bayan ya daɗe yana yin watsi da ita, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa El-Rufai ya manta da tsarin raba iko wanda ke cikin kundin tsarin mulki, wanda ya hana yin katsalandan a tsakanin ɓangarorin zartaswa, majalisa da shari'a.

"Shin (El-Rufai) yana ganin ta hanyar kai ƙara zai iya kawo wa majalisa cikas wajen gudanar da ayyukanta na tsarin mulki?"

- Mahmud Lawal

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauki mataki kan sabon mafi ƙarancin albashi a taron majalisar zartarwa

An zargi El-Rufai da karkatar da kuɗaɗe

Ɗan majalisar ya bayyana cewa jihar Kaduna ba ta taba fuskantar cin hanci da rashawa ba kamar yadda aka gani a mulkin El-Rufai inda aka karkatar da kuɗaɗe da sunan aiwatar da ayyuka.

"Misali, bari in kwatanta abin da ya faru a Kofar Doka a Zaria, mazaɓa ta. An ce an ware biliyoyin Naira domin gudanar da ayyukan tituna."
"Amma abin takaici, abin da ake iya gani kawai shi ne buldoza na ruguza gidajen jama’a, inda suka zama marasa matsuguni."

El-Rufai ya garzaya zuwa kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Nasir Ahmad El-Rufai ya maka majalisar dokokin jihar Kaduna a kotu kan zarginsa da ta yi da karkatar da N432bn a shekaru takwas na mulkinsa da kuma barin ɗimbin bashi.

Tsohon gwamnan ya shigar da ƙara kan take ƴanci a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna, inda ya ke ƙarar majalisar dokokin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng