Gwamna Ya Faɗi Sunan Wanda Ya Tayar da Bam, Ya Alakanta Shi da Ministan Tinubu
- Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana sunan wanda ya tashi bam da nufin kara tayar da hargitsi a jihar Ribas lokacin zanga-zanga
- Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Nelson Chukwudi ya ce mutumin, Josiah Preye ya kammala karatun Jami'a kuma ɗan tsagin Wike ne
- Ya kuma kafa hujja da faifan bidiyon wanda ake zargin a cikin masu zanga-zanga da kuma lokacin da yake jinya a asibiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Gwamnatin jihar Ribas karkashin Gwamna Siminalayi Fubara ta bayyana sunan wanda ake zargi da tayar da bam a Fatakwal a ranar Talata.
Gwamnatin ta bayyana sunansa da Josiah Preye, wanda ya kammala karatu a jami'a kuma yana rayuwa gami da aiki a Fatakwal, babban birnin jihar.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran Gwamna Fubara, Nelson Chukwudi ya fitar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Siminalayi Fubara ya jaddada cewa wanda ake zargi da yunkurin tayar bam ɗin ɗan tsagin ministan babban birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ne.
Yadda lamarin ya faru a Rivers
Idan ba ku manta ba, wani abin fashewa ya tashi a kusa da katafaren otal a Fatakwal a lokacin da ake zanga-zanga kan canza shugabannin ƙananan hukumomi a Fatakwal.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa abun fashewar ya tashi da wanda ake zargin tun kafin ya ida nufinsa, kuma yanzu haka jami'an tsaro na tsare da shi a asibiti.
Bayan haka ne Gwamna Fubara ya fito ya ɗora laifin kan magoya bayan Wike, inda ya ce sun shirya tayar da bam din ne domin a ayyana dokar ta ɓaci a jihar, Premium Times ta rahoto.
Fubara ya saki bayanan wanda ake zargi
Sanarwar da sakataren yaɗa labaran gwamnan ya fitar ta yi bayanin cewa wanda ake zargin na cikin masu zanga-zangar goyon bayan Wike a ranar Talata.
Gwamnatin Fubara ta kafa hujja da faifan bidiyon wani a cikin masu zanga-zanga rufe da fuska wanda ta ce shi ne wanda ake zargi da bidiyon wanda ke jinya a asibiti.
Gwamna Fubara ya soki PDP
A wani rahoton kuma Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana rashin jin dadinsa ga jam'iyyar PDP inda ya ce ta gaza a jihar Rivers.
Gwamna Fubara ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta gaza wajen cimma muradunsa da magoya bayansa a jihar da ke Kudancin Najeriya.
Asali: Legit.ng