Gwamnan Edo: PDP Ta Ce An Toshewa APC Hanyar Maguɗi, Ta Fadi Yadda Za Ta Ci Zaɓe

Gwamnan Edo: PDP Ta Ce An Toshewa APC Hanyar Maguɗi, Ta Fadi Yadda Za Ta Ci Zaɓe

  • Jam'iyyun siyasa na cigaba da daura damara wajen neman hadin kan masu zabe yayin da ake daf da yin zaɓen gwamna a jihar Edo
  • Shugabannin jam'iyyar PDP sun bayyana irin shirin da suka yi domin ganin sun samu nasara kan jam'iyyar APC cikin sauki a yayin zaben
  • Har ila yau, PDP ta bayyana yadda aka toshe hanyar da za a samu damar yin maguɗi ko aringizon kuri'u a yayin zaben wannan karon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Shugabannin jam'iyyar PDP sun yi gangami yayin da zaɓen gwamna a jihar Edo ke kara matsowa kusa.

Jam'iyyar PDP ta ce a wannan karon za ta tabbatar da samun nasara kan APC a jihohin Edo da Ondo.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta da shari’ar zabe ba su taka masa burki ba, an nada Abba gwarzon Gwamnoni

PDP in Edo
PDP ta ce za ta lashe zaben Edo. Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri da muƙaddashin shugaban PDP, Iliya Damagun ne suka yi bayanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An toshe hanyar maguɗin APC" - PDP

Yayin da yake bayani, gwamnan jihar Adamawa ya bayyana cewa sanya kimiyyar zamani cikin harkokin zabe zai hana yin maguɗi.

Ahmadu Fintiri ya kara da cewa suna da kwarin gwiwa a kan dan takararsu na jihar Edo saboda ayyukan cigaba da ya kawo jihar.

PDP ta ce Edo ba Legas ba ce

Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP, Iliya Damagun ya ce shugaba Bola Tinubu ba zai yi tasiri a zaben jihar Edo ba.

Damagun ya bayyana haka ne inda yake cewa dama tun asali akwai taken cewa jihar Edo ba Legas ba ce kuma hakan zai yi aiki a wannan karon.

Edo: PDP ba za ta yi wasa ba

Kara karanta wannan

Ganduje ya ga ta kansa, wasu manyan jiga jigai da mambobin APC sun koma PDP

Shugaban PDP ya kara da cewa a wannan karon jam'iyyar ta shirya tsaf domin samun nasara a zaben da za a gudanar, rahoton Punch.

Ambasada Damagun ya kuma tabbatarwa jam'iyyar APC cewa abu ne mai matukar wahala gareta ta samu jihar Edo musamman yadda dan takarar PDP ya samu karɓuwa.

A ranar 21 ga watan Satumba mai zuwa ne hukumar INEC ta ayyana cewa za a yi zaben gwamna a jihar Edo.

APC ta yi alwashin cin zabe a Edo

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana aniyarta na samun karin gwamnonin jihohi a kudancin Najeriya.

Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a birnin Kalaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel