Bukatar Bola Tinubu Ta Jawo Zazzafar Muhawara a Majalisar Tarayya, Hayaniya Ta Ɓarke
- Ƴan majalisar wakilan tarayya sun yi zazzafar muhawara a tsakaninsu kan buƙatar da Bola Tinubu ya aiko ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni, 2024
- Mambobin majalisar sun tafka zazzafan kace-nace kan buƙatar Tinubu na tsawaita lokacin aiwatar da kasafin 2023 zuwa watan Disamba
- Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya ce ba daidai ba ne a ce kasar nan na tafiyar da kasafin kudi uku zuwa hudu a lokaci guda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Buƙatar da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya tura majalisar wakilai ta haifar da zazzafar muhawara a zaman yau Alhamis, 27 ga watan Yuni, 2024.
Shugaba Tinubu ya buƙaci majalisar ta tsawaita wa'adin aiwatar da kasafin 2023 na N23.83trn da ƙarin kasafin 2023 na N2.17 zuwa watan Disamba.
Buƙatar Tinubu ta tayar da hayaniya
Sai dai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, lamarin bai kwanta ma shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda ba, nan take ya tashi ya nuna damuwarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Honorabul Chinda ya nuna damuwa da cewa a hankalce ba daidai ba ne a ce ƙasa ta tasa kasafin kuɗi guda uku zuwa huɗu tana aiwatar da su a lokaci guda.
Dan majalisar PDP daga jihar Ribas ya bada shawarar cewa maimakon tsawaita lokacin, kamata ya yi a ɗauki muhimman ayyuka da ke cikin karin kasafin a haɗe su a babban kasafin 2023.
Tajudeen ya ɗauki mataki
Duk da rokon da kakakin majalisar Abbas Tajudeen ya yi, yawancin ‘yan majalisar sun nuna ba su yarda da tsawaita kasafin ba, inda suka ci gaba da nanata a'a.
A rahoton Premium Times, mambobin jam'iyyun adawa sun tayar da hayaniya domin hana kakakin majalisar Tajudeen shawo kan lamarin.
Daga nan Tajuddeen ya ayyana shiga zamam sirri domin ƴan majalisar su fahimci lamarin kuma su warware batutuwan kafin ci gaba da duba kudirori.
Shettima da gwamnoni sun sa labule
A wani rahoton na daban Sanata Kashim Shettima da gwamnoni sun sa labule a fadar shugaban kasa da ke Abuja kan muhimman batutuwa.
Mataimakin shugaban ƙasar ne ke jagorantar taron wanda ke gudana karkashin majalisar tattalin arzikin ƙasa (NEC).
Asali: Legit.ng