Gwamna Ya Yi Magana Kan Yunƙurin Tashin Bam, Ya Fallasa Masu Ɗaukar Nauyi

Gwamna Ya Yi Magana Kan Yunƙurin Tashin Bam, Ya Fallasa Masu Ɗaukar Nauyi

  • Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya zargi wasu mutane da hannu a kokarin tashin bam a birnin Fatakwal
  • Fubara ya bayyana cewa an shirya tayar da bam ne domin a jawo hankalin gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta ɓaci a Ribas
  • Ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya karɓi bakuncin mambobin kwamitin majalisar dattawa kan kamfanoni a fadar gwamnatinsa ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya yi zargin cewa yunkurin dasa bam a jihar na da alaƙa da masu kiran a ayyana dokar ta ɓaci a jihar.

Fubara ya zargi magoya bayan tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike da shirya makircin tashin bam a wani babban Otal a birnin Fatakwal.S

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware miliyoyi kan kiwon lafiya, ta yi albishir ga masu cutar sikila

Gwamna Fubara na Rivers
Gwamna Fubara ya ce an yi kokarin dasa bam a Fatakwal ne domin hargiza jihar Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Gwamnan ya ayyana magoyan bayan Nyesom Wike da yake zargi a matsayin maƙiya, waɗanda ke kokarin warzaga zaman lafiyar Ribas domin cimma burinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Gwamna Fubara ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin kwamitin majalisar dattawa mai kula da kamfanoni da kasuwanci.

Ya karɓi bakuncin kwamitin karkashin jagorancin shugaba, Sanata Orji Uzo Kalu a gidan gwamnatin Ribas da ke Fatakwal ranar Laraba, 26 ga watan Yuni, 2024.

Fubara ya fallasa waɗanda yake zargi

A jawabinsa, Gwamna Fubara ya ce wasu marasa son zaman lafiya ne suka ɗauki hayar matasa domin su gudanar da zanga-zangar neman ƙara wa'adin tsofaffin ciyamomi.

Ya ƙara da cewa masu zanga-zangar da masu ɗaukar nauyinsu sun san cewa akwai ƴan majalisar tarayya a cikin otal ɗin amma suka yi kokarin dasa bam a kusa da wurin.

Kara karanta wannan

Mutuwar jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu ya aikawa Iiyalin Marigayi Etop Essien saƙo

Sun yi haka ne ba don komai ba sai domin gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta ɓaci a jihar, kamar yadda PM News ta tattaro shi.

Fubara ya ce:

"A gaskiya, bari in gaya muku, na san duk abin da ya faru jiya (Talata), sun san cewa kuna cikin jihar nan shiyasa suka yi ƙoƙarin tayar da hargitsi.
"Hasali ma an yi nufin tashin bam a otal din da mutane ke ciki amma Allah ya kare, makircin ya koma kan wanda ya yi kokarin dasa bam din, ya tashi da hannunsa."

MURIC ta nanata yunkurin tsige Sultan

A wani labarin kun ji cewa kungiyar Musuluncin nan MURIC ta sake nanata cewa Gwamnatin Sokoto na shirin sauke Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III.

Ta ce dokar masarautun da majalisar dokokin Sokoto ke sauri-saurin aiki a kanta wani yunƙuri ne na rage karfin ikon fadar Sarkin Musulmi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262