Bayan Manyan Arewa Sun Taru a Katsina, Gwamnonin Kudu Sun Shiga Ganawa a Ogun
- A yau Litinin, 24 ga watan Yuni daukacin gwamnonin kudancin Najeriya suka taru a jihar Ogun da ke kudu maso yamma domin ganawa
- Rahotanni sun nuna cewa za a yi taron ne a masaukin shugaban kasa na jihar Ogun da ke rukunin gidajen Ibara a birnin Abeokuta
- Gwamnatin jihar Ogun karkashin jagorancin gwamna Dapo Abiodun ta sanar da isowar wasu daga cikin gwamnonin yankin domin ganawar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ogun - A yau Litinin ne gwamnonin Kudancin Najeriya za su yi taro na musamman a birnin Abeokuta na jihar Ogun.
Mai masaukin baki, gwamnatin jihar Ogun ta sanar da cewa a yanzu haka wasu daga cikin gwamnoni sun isa filin taron.
Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin wani sako da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin Kudu da suka isa wajen taron
Gwamnatin jihar Ogun kuma mai masaukin baki ta tabbatar da cewa gwamnoni 10 sun fara isa wajen taron.
Cikin gwamnonin da suka isa akwai gwamnonin Legas, Oyo, Ekiti, Abia, Edo, Osun, Cross River, Imo Delta da Ondo.
Makasudin taron gwamnonin jihohin Kudu
Duk da cewa gwamnoni ba su bayyana dalilin taron ba, jaridar Daily Trust ta yi hasashen cewa za su iya zaben shugaban su a wajen taron.
Tun bayan rasuwar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu wanda shi ne tsohon shugaban kungiyar, gwamnonin ba su sake taro ba sai yau Litinin.
Har ila yau ana tsammanin dukkan gwamnonin jihohin Kudu su 17 za su halarci taron na yau a jihar Ogun.
Ana taron shawo matsalar tsaro a Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa damuwa kan yadda matsalar tsaro ta hana jama'ar Arewacin Najeriya sakat, za a gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a jihar Katsina a yau Asabar
Rahotanni na nuni da cewa wannan shi ne karon farko da za a gudanar da babban taro irin wannan a Arewa duk da kalubalen rashin tsaro da ya addabi al'umar yankin na tsawon shekaru.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng