Gwamna Ya Nuna Yatsa Kan 'Yan Majalisar da Ke Adawa da Shi

Gwamna Ya Nuna Yatsa Kan 'Yan Majalisar da Ke Adawa da Shi

  • Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya zargi wasu ƴan majalisar tarayya a jihar da nuna adawa da shirinsa na kawo ci gaba a jihar da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Gwamnan wanda bai ambaci suna ba dai ya yi bayanin cewa ƴan majalisar ba za su iya kawo masa cikas ba a shirinsa na kawo ci gaban
  • Kalaman gwamnan dai ba su rasa nasaba da yadda dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, inda wasu ƴan majalisa ke goyon bayansa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya zargi ƴan majalisar tarayya daga mazaɓar Gwer/Gwer ta jihar Benue da nuna adawa da shirinsa na ci gaban jihar.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarauta, ƴan bindiga sun kai hari Masallaci, sun sace basarake

Gwamna Hyacinth Alia ya yi wannan zargin ne yayin ziyarar ban godiya da ya kai ga mutanen Gwer a karshen mako.

Gwamnan Benue ya nuna yatsa ga wasu 'yan majalisa
Gwamna Hyacinth Alia ya zargi wasu 'yan majalisa da yin adawa da shi Hoto: Hyacinth Alia
Asali: Facebook

Wane zargi Gwamna Alia ya yi?

Gwamnan na jihar Benue ya yi jawabi ne a wajen taron da aka gudanar a makarantar firamare ta St. Francis da ke Aliade a ƙaramar hukumar Gwer ta Gabas, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da gwamnan bai ambaci suna ba, ƴan majalisar tarayya da ke yankin sune Sanata Titus Zam na Benue ta Arewa ta Yamma da Arc. Asema Achado, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Gwer ta Gabas/Gwer ta Yamma.

Mutanen biyu magoya bayan sakataren gwamnatin tarayya ne, Sanata George Akume, wanda ke da danganta mai tsami da Gwamna Alia saboda iko kan jam'iyyar APC a jihar.

Gwamna Alia a lokacin ziyarar dai ya yi nuni da cewa ƴan majalisar tarayyan na adawa da shirye-shiryensa na cigaba amma ya ba su tabbacin cewa ba za su kawo cikas kan ƙudirinsa ba.

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki, 'yan bindiga sun hallaka Amarya mako 1 tak bayan ɗaura aurenta

Gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda suka ƙi ba shi goyon bayan da ya dace domin kawo ci gaba ga al'ummar jihar Benue, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.

Kotu ta hana Gwamna Alia binciken Ortom

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun jiha a Makurdi ta dakatar da Gwamna Alia Hyacinth binciken tsohon gwmanan jihar, Samuel Ortom.

Kotun ta ɗauki wannan matakin ne a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu inda ta ce kwamitin da aka kafa ya dakatar da binciken da ake yi kan tsohon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng