Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tanadi Hukunci Kan Tsige Ƴan Majalisa 27 da Suka Bar PDP Zuwa APC

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tanadi Hukunci Kan Tsige Ƴan Majalisa 27 da Suka Bar PDP Zuwa APC

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta kammala zaman sauraron shari'ar tsige 'yan majalisar dokokin Ribas waɗanda ke goyon bayan Nyesom Wike
  • A zaman ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024, kotun ta tanadi hukunci kan ƙarar inda ta ce za ta sanar da sanar yanke hukunci
  • Tun farko dai babbar kotun Ribas ta kori ƴan majalisar da ke ƙarƙashin shugabancin Martin Amaewhule saboda sun sauya sheka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Fatakwal ta shirya yanke hukunci a shari'ar tsige Martin Amaewhule da sauran 'yan majalisar dokokin jihar Ribas 26.

Ana gwabza shari'a ne tsakanin ƴan majalisa 27 karkashin jagorancin Rt. Hon. Martin Amaewhule da kuma ƴan majalisar da ke karƙashin Victor Oko Jumbo.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi magana yayin da ake jiran yanke Hukunci kan sahihancin tuɓe Sarkin Kano

Kotun ɗaukaka kara da Martin Amaewhule.
Kotun ɗaukaka kara ta tanadi hukunci a karar tsige ƴan majalisa na tsagin Wike a Ribas Hoto: @DeeoneAyekooto/officialPDPNig
Asali: Twitter

Honorabul Amaewhule, tsohon kakakin majalisar dokokin Ribas ne ya shigar da ƙara tare da wasu mutum 24, inda suka kalubalanci tsagin Mista Jumbo, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda zaman kotu ya gudana

A zaman shari'ar na yau Alhamis, tsagin masu ƙara sun roƙi kotun ta jingine hukuncin da babbar kotun jiha ta yanke na tsige su daga matsayin ƴan majalisar Ribas.

Haka nan kuma sun roƙi kotun ta soke duk wani mataki da majalisar dokoki karkashin Jumbo ta ɗauka.

Sun kuma buƙaci kotun ɗaukaka karar ta hanzarta kammala sauraron wannan ƙara, sannan sun zargi ƙaramar kotu ta shiga hurumin da ba nata ba.

'Yan majalisar Rivers za su san matsayarsu

Bayan sauraron bayanan lauyoyin kowane ɓangare, kwamitin mutum uku karkashin jagorancin mai shari’a Jimi Olukayode-Bada ya tanadi hukunci.

Ya ce za a sanar da kowane ɓangare ranar da za a dawo domin yanke hukunci kan batun a nan gaba, The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi magana yayin da kotu ke shirin sanar da halataccen Sarkin Kano

Rikicin Rivers: Yadda shari'ar ta faro

Idna ba ku manta ba a ranar 14 ga watan Yuni, kotun ɗaukaka ƙara ta umarci kowane ɓangare ya riƙe matsayinsa har zuwa lokacin yanke hukunci.

Kotun daukaka kara ta kuma dakatar da babbar kotun jiha ko wata kotu daga sauraron wannan ƙara har sai ta yanke hukunci.

An samu jinkiri a shari'ar sarautar Kano

A wani rahoton kun ji cewa an samu jinkirin yanke hukunci kan sahihancin sabuwar dokar masarautar Kano wadda ta sauke sarakuna biyar kuma ta mayar da Muhammadu Sanusi II.

Magatakardar Babban Kotun Tarayya mai zama a Kano ya sanar da ɗage zaman yanke hukuncin zuwa ƙarfe 2:00 na tsakar rana yau Alhamis.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel