Rigima Ta Ƙara Tsanani, APC Ta Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Jiha 1

Rigima Ta Ƙara Tsanani, APC Ta Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Jiha 1

  • Yayin da rikici ke kara ƙamari a jihar Ribas, APC ta yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci domin kawo karshen kashe-kashen rayuka
  • Shugaban APC na rikon kwarya a jihar, Tony Okocha ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan Gwamna Fubara ya rantsar da sababbin ciyamomi
  • Ya kuma nesanta jam'iyyar APC da kalaman tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi wanda ya ce ƴan Najeriya ba za su zaɓi Tinubu ba a 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Jam'iyyar APC ta reshen jihar Ribas ta yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci.

APC ta buƙaci shugaban kasa ya ɗauki wannan matakin ne saboda rikicin da ya ɓarke a jihar Ribas bayan karewar wa'adin shugabannin ƙananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Kano: NNPP tayi martani, ta ce APC na yunƙurin ƙwace mulki daga Gwamna Abba

APC da Gwamna Fubara.
APC ta buƙaci Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihar Rivers Hoto: APC Nigeria, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

APC tana son dokar ta baci a Ribas

Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta jihar, Tony Okocha ya ce matakin zai daƙile kashe-kashen rayuka da kuma kawo ƙarshen rikicin da ke ƙara ta'azzara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kira na APC na zuwa ne jim kaɗan bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya rantsar da kantomomi 23 ranar Laraba, 19 ga watan Yuni a cewar The Nation.

Fubara ya maye gurbin ciyamomi 23

Idan ba ku manta ba Gwamna Fubara ya maye gurbin shugabannin ƙananan hukumomin da ke goyon bayan ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Kashi na farko na kantomomi 11 watau shugabannin kananan hukumomi na riƙon kwarya sun karɓi rantsuwar kama aiki a fadar gwamnatin Ribas yau Laraba.

Da yake martani kan halin da ake ciki, shugaban APC ya bayyana cewa jihar Ribas na cikin babbar matsala kuma gwamna ya gaza kataɓus.

Kara karanta wannan

An miƙa wa Bola Tinubu sunan wanda ya kamata ya naɗa a matsayin ministan jin ƙai

APC ta aika saƙo ga Bola Tinubu

"Yaƙi na neman ɓarkewa a Ribas kuma waɗanda suka kitsa lamarin sun fara jawo asarar rayuka, gwamna da ƴan sanda sun gaza kataɓus.
"Saboda haka jam’iyyar APC a jihar Ribas na kira da a kafa dokar ta-baci a jihar domin magance tarzoma da tada zaune tsaye a jihar."

- Tony Okocha.

Ya kuma nesanta jam'iyyar APC da kalaman tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya ce ƴan Najeriya sun shiga taitayinsu.

Ana zargin Amaechi ya ce jama'a ba za su zaɓi Tinubu ba a 2027, Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Fubara ya sallami ciyamomi 23

Tun farko rahoto ya zo cewa Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya sallami duka shugabannin kananan hukumomi a jihar.

Fubara ya umarci shugabannin gudanarwa da su karbi ragamar shugabancin bayan karewar wa'adin ciyamomin waɗanda ke goyon bayan ministan Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262