Mataimakin Gwamnan da Aka Tsige da Ɗan Majalisar Tarayya Sun Koma Bayan APC
- Mataimakin gwamnan jihar Edo da aka tsige, Philip Shaibu da tsohon ɗan majalisar tarayya sun koma bayan jam'iyyar APC
- Manyan jiga-jigan biyu sun bayar da gudummuwa mai tsoka ga kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar APC, Monday Okpebolo
- Ranar 21 ga watan Satumba, 2024 hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) za ta gudanar da zaɓen gwamna a jihar Edo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Tsofaffin ƴan takarar da suka nemi tikitin PDP, Philip Shaibu da Hon. Omoregbe Ogbeide-Ihama, sun koma bayan jam'iyyar APC.
Shaibu, shi ne mataimakin gwamnan jihar Edo wanda majalisar dokokin jihar ta sauke daga muƙaminsa bayan kammala zaɓen fidda ɗan takarar jam'iyyar PDP.
Daily Trust ta ruwaito cewa Shaibu da Ogbeide-Ihama sun bayar da gudumuwa ga kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan APC, Sanata Monday Okpebolo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jiga-jigan biyu sun nemi tikitin takarar gwamna a inuwar PDP amma suka sha kaye a hannun Asue Ighodalo, wanda Gwamna Godwin Obaseki ya marawa baya.
Wace gudummuwa suka ba APC?
A nasa bangaren, Shaibu, ya bayar da gudummawar motocin bas Toyota Sienna sama da 50, kayan kiɗa, da ofishin yakin neman zabensa ga kwamitin kamfen Okpebolo/DENCO.
Haka nan Ogbeide-Ihama, tsohon ɗan majalisar wakilai har sau biyu, ya bayar da kyautar ofishin yakin neman zabe ga jam’iyyar APC.
Dukkan ofisoshin biyu suna tsakiyar birnin Benin, kuma zasu zama cibiyar tsara harkokin kamfen APC da kuma ganawa da mutane, PM News ta tattaro.
Daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaben APC a jihar Edo, Osigwe Omo-Ikirodah, ya tabbatar da karɓar gudummuwa daga ƴan siyasar biyu.
"Yadda Shaibu da Ogbeide-Ihama suka marawa APC baya ka iya jawo wasu mambobin PDP su sake tunani, su dawo goyon bayan jam'iyyarmu."
Wannan na zuwa ne yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar Edo wanda za a yi ranar 21 ga watan Satumba, 2024.
Gwamna Buni ya biya albashin Yuni
A wani rahoton kuma yayin da ake shirin babbar Sallah, Gwamna Mai Mala Buni ya umarci a biya ma'aikatan gwamnati albashin watan Yuni a Yobe.
Babban sakataren hukumar kula da ma'aikata na jihar, Alhaji Bukar Kilo ne ya bayyana haka a madadin shugaban ma'aikatan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng