Neja: Abubuwan Sun Rikice a APC, An Dakatar da Shugabar Mata a Arewa

Neja: Abubuwan Sun Rikice a APC, An Dakatar da Shugabar Mata a Arewa

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da mataimakiyar shugabar matan jam'iyyar ta jihar Neja, Sayyada Amina Shehu na tsawon watanni shida
  • Sakataren watsa labarai na APC reshen jihar Neja, Musa D Sarkinkaji ne ya bayyana haka, ya ce an ɗauki matakin ne bayan gudanar da bincike
  • Har yanzun dai mataimakiyar shugabar matan ba ta mayar da martani kan lamarin ba, amma APC ta ce ta bi duk matakan da suka dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC reshen jihar Neja, ya dakatar da mataimakiyar shugabar mata ta jihar, Sayyada Amina Shehu.

Jam'iyya mai mulki ta dakatar da Sayyada Amina na tsawon watanni shida bisa zarginta da hannu a wata badaƙalar bayar da muƙami.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ɗauki zafi, an dakatar da wasu manyan jiga jigan jam'iyya

Shugaban APC Ganduje.
Jam'iyyar APC ta dakatar da mataimakiyar shugabar mata a jihar Neja Hoto: Official APC
Asali: Twitter

An hukunta shugabar mata a jam'iyyar APC

Sakataren watsa labarai na APC ta reshen jihar Neja, Musa D. Sarkinkaji, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kwamitin ayyuka na APC ya dogara da wasu tanade-tanaden kundin tafiyar da harkokin jam'iyyar wajen dakatar da shugabar matan, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Meyasa APC ta dakatar da Sayyada Amina?

Sarkinkaji ya bayyana cewa an dakatar da mataimakiyar shugabar matan dogaro da tanadin sashe na 21 (5) xii da ke cikin kundin tsarin mulkin APC na 2022 wanda aka yiwa garambawul.

Ya bayyana cewa tun da farko jam’iyyar APC ta kafa kwamitin bincike na mutum biyar karkashin jagorancin mataimakin shugaba na jihar, Zakariyau Umar Raba.

A cewarsa, an kafa wannan kwamiti ne ba don komai ba sai don ya yi bincike kan zargin da ake wa Sayyada Amina Shehu, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya bayyana abin da ke kokarin wargaza jam'iyyar a Najeriya

Sai dai har kawo yanzu da muke haɗa maku wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin Sayyada Amina ba domin jin matsayarta kan dakatarwan.

APC ta dakatar da wasu kusoshi a Abia

A wani rahoton na daban ga dukkan alamu rigima na neman ɓarkewa a jam'iyyar APC reshen jihar Abia a lokacin da aka dakatar da wasu manyan jiga-jigai.

Masu ruwa da tsakin APC a Aba ta Arewa sun yanke shawarar dakatar da wasu mambobi bisa zargin rashin ɗa'a, ladabi da kuma sojan gona.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262