Ganduje Ya Bayyana Hanyar da APC Za Ta Rika Bi Wajen Ba da Mukamai

Ganduje Ya Bayyana Hanyar da APC Za Ta Rika Bi Wajen Ba da Mukamai

  • Jam'iyyar APC ta fara shirin yiwa mambobinta rajista ta yanar gizo domin ta san adadin yawan da suke da shi a faɗin ƙasar nan
  • Shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa za a riƙa amfaniɓda rajistar wajen ba da muƙamai a kowane mataki
  • Wannan ne dai karo na farko da jam'iyyar APC wacce ke mulkin Najeriya ta kawo tsarin yiwa mambobinta rajista ta yanar gizo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana hanyar da jam'iyyar za ta riƙa bi wajen ba da muƙamai.

Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar za ta riƙa amfani da rajistar mambobinta ta yanar gizo domin yin naɗe-naɗe na siyasa a kowane mataki.

Kara karanta wannan

PDP ta watsawa Atiku ƙasa a ido kan hadaka da Kwankwaso, Obi, ta yi alfahari

Ganduje ya yi magana kan samun mukamai a APC
Ganduje ya fadi amfanin yin rajistar yanar gizo ta APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

APC: Me Ganduje ya ce kan samun muƙami?

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da buɗe taron bita na horar da waɗanda za su horar da masu aikin yin rajistar yanar gizo na jam'iyyar APC a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa samun shaidar yin rajistar ta yanar gizo da jam'iyyar, shi ne abin da zai sanya mamba ya samu damar yin taƙara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar, rahoton jaridar Daily Nigerian ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa ƴan Najeriyan da suke son yin rajista da jam'iyyar a matsayin mambobi, za su kawo bayanansu waɗanda suka yi daidai da na katin shaidar zama ɗan ƙasa (NIN).

Maganar shugaban APC, Abdullahi Ganduje

"A yau cikin yardar Allah mun taru a nan domin cika alƙawarin da muka ɗauka na fara tsarin mayar da rajistar jam'iyyarmu na zamani."

Kara karanta wannan

Duk da umarnin sammaci, Ganduje ya yi biris, ya kaddamar da muhimmin aiki ga APC

"Wannan ƙoƙari ne na samun adadin yawan mambobin jam'iyyarmu da yankunan da suka fito."
"Hakan zai zama madogara da za a duba kan kowane mamba da ke neman muƙami a kowane mataki ko neman tsayawa takara."

- Abdullahi Umar Ganduje

Batun neman tsige Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sanya ranar fara sauraron ƙarar neman tsige Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC.

Kotun ta sanya ranar, 13 ga watan Yuni domin sauraron ƙarar da ke neman a tsige tsohon gwamnan na jihar Kano daga shugabancin APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng