APC Ta Yi Hannun Riga da Wani Tsohon Gwamna, Ta Cire Shi Daga Jagororin Jam’iyya
- Jam’iyyar APC reshen jihar Osun ta kai karar Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan jihar ga kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa
- APC ta zargi Aregbesola, wanda tsohon ministan Najeriya ne da kafa kungiyoyi da ke gudanar da ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar a jihar
- Shugaban APC na jihar, Tajudeen Lawal ya gargadi 'yayan jam'iyyar da su kiyayi alaka da Aregbesola kasancewar yanzu ba su tare
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Osun - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Osun ta yi hannun riga da tsohon gwamnan jihar, Rauf Aregbesola.
Shugaban jam’iyyar APC a Osun,, Tajudeen Lawal ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa bayan taron masu ruwa da tsaki na jiya a sakatariyar jihar da ke Osogbo.
APC ta nesanta kanta da Aregbesola
Shugaban ya ce tsohon ministan harkokin cikin gida ya tafka ayyuka daban-daban na adawa da jam’iyyar da suka hada da kirkirar kungiyoyi ba tare da izini ba, in ji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi kungiyar Aregbesola mai suna Omoluabi Progressives da fara yiwa mutane rijista a gundumarsa tun gabanin jam'iyyar ta APC ta fara rijistar ta hanyar na’ura mai kwakwalwa.
Tajudeen Lawal ya ja kunnen ‘ya’yan jam’iyyar da kada a yaudare su su yi rajista da tsohon gwamnan saboda APC ba ta da alaka da wannan kungiya.
Ganduje zai kaddamar da kwamitin APC
Jaridar Vanguard ta ruwaito jam’iyyar ta APC ta kuma bayyana cewa ta kai karar Rauf Aregbesola ga kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa a kan ayyukan zagon kasa.
Sakataren jam’iyyar APC a jihar, Kamoru Alao, wanda ya tabbatar da kalaman shugaban jam’iyyar ya ce gobe ne za a fara rijistar mambobin jam’iyyar.
Ya ce shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje ne zai kaddamar da kwamitin da zai horas da masu yin rijistar a matakin kananan hukumomi.
Tinubu ya karrama Wole Soyinka
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya karrama babban marubucin Najeriya, Wole Soyinka ta hanyar sanya sunansa a jikin babbar hanyar Abuja.
Shugaba Bola Tinubu ya ce hanyar N20 ta Abuja ta ci sunan Wole Soyinka saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar da harkar dab'i da jawo wa Najeriya farin jini a idon duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng