Shugabancin APC: Kotu Ta Sanya Ranar Sauraron Karar Neman Tsige Ganduje

Shugabancin APC: Kotu Ta Sanya Ranar Sauraron Karar Neman Tsige Ganduje

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta tsayar da ranar da za ta fara sauraron ƙarar da aka shigar kan Abdullahi Umar Ganduje
  • Alƙalin kotun mai shari'a Inyang Ekwo ya sanya ranar, 13 ga watan Yuni domin fara sauraron ƙarar wacce ke neman a tsige Ganduje daga shugabancin APC
  • Masu shigar da ƙarar sun buƙaci kotun da ta hana Ganduje bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sanya ranar fara sauraron ƙarar neman tsige Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC.

Kotun ta sanya ranar, 13 ga watan Yuni domin sauraron ƙarar wacce ke neman a tsige tsohon gwamnan na jihar Kano daga shugabancin APC.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan APC 25, ta hana su ayyana kansu a matsayin 'yan majalisa

Kotu ta sanya ranar sauraron karar da aka shigar da Ganduje
Masu shigar da karar na son a tsige Ganduje daga shugabancin APC Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Tsige Ganduje: Yaushe za a saurari ƙarar?

Jaridar The Nation ta ce ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/599/2024, wata ƙungiya ce mai suna 'North Central APC' ƙarkashin jagorancin Saleh Zazzaga ta shigar da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Inyang Ekwo shi ne ya sanya ranar yayin zaman kotun na ranar Alhamis, 30 ga watan Mayun 2024 bayan ya fahimci cewa dukkanin ɓangarorin biyu da ke cikin shari'ar ba su gabatar da takardun da ake buƙata ba.

Mai shari'a Enyang Ekwo ya ɗage ƙarar zuwa ranar, 13 ga watan Yuni domin fara sauraronta da ƙorafin da waɗanda ake ƙara za su gabatar, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Me masu shigar da ƙarar suke so?

Masu shigar da ƙarar sun buƙaci kotu da ta hana Ganduje bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa.

Suna kuma son kotun ta ba da umarni ga hukumar zaɓe ta INEC da kada ta amince da duk wani mataki da jam'iyyar APC ta ɗauka tun bayan da Ganduje ya zama shugaban APC a ranar, 3 ga watan Agustan 2023.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: 'Yan majalisan Kano 12 sun yi mubaya'a ga Sarki na 15

Masu shigar da ƙarar na ganin cewa zama Ganduje a kujerar shugabancin APC ya saɓawa kundin tsarin mulkin jam'iyyar saboda bai fito daga yankin Arewa ta Tsakiya ba.

Batun dakatar da Ganduje a APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar shugabannin jam'iyyar APC na jihohi ta kaɗa ƙuri’ar amincewa da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje.

Tawagar wakilan shugabannnin APC na jihohi 36 da Abuja ne suka tabbatar da goyon bayansu ga Ganduje yayin da suka kai masa ziyara hedkwatar APC da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel