Ana Tsaka da Rigimar Sarauta, Gwamnatin Tinubu Ta Sa Tushen Muhimmin Aiki a Kano

Ana Tsaka da Rigimar Sarauta, Gwamnatin Tinubu Ta Sa Tushen Muhimmin Aiki a Kano

  • Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta sanya tushen gina gidaje a kauyen Lambu, ƙaramar hukumar Tofa a jihar Kano
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa shugaban ƙasa bisa yadda ya jajirce domin cike giɓin ƙarancin gidaje a ƙasar nan
  • Ministan gidaje da raya birane na ƙasa, Arc Ahmad Ɗangiwa, ya ce a kashin farko gwamnati za ta gina gidaje 50,000 a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Yayin da ake taƙaddama kan sarauta, gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu ta sa tushen gina gidaje 500 a jihar Kano.

Gwamnatin ta hannun ma'aikatar gidaje da raya birane ta fara gina gidajen a wani ɓangare na shirin gina rukunin gidajen sabunta fatan ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dakatar da muhimmin aikin da Buhari ya fara a Najeriya

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin tarayya ta fara gina gidaje a jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnan Kano ya yabawa Tinubu

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci bikin sanya tushen ginin tare da Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ministan gidaje da raya birane, a kauyen Lambu da ke karamar hukumar Tofa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton da Daily Trust ta kawo, Gwamna Abba ya godewa shugaban kasa Bola Tinubu bisa ƙoƙarinsa wajen magance matsalar rashin isassun gidaje a Najeriya.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa shirin zai taimaka wajen dakile ƙaruwar gina gidaje ba bisa ƙa'ida ba da kuma rage karancin gidaje a jihar Kano.

Za a gina gidaje 500 a Kano

A nasa jawabin, ministan gidaje da raya birane, Ɗangiwa ya ce rukunin gidajen da gwamnatin za ta gina a Kano zai kunshi gidaje masu ɗakin kwana ɗaya guda 100.

Bayan haka birnin sabunta fatan zai kuma haɗa da gidaje masu ɗakunan kwana biyu guda 300 da kuma gidaje masu ɗakunan kwana uku guda 100, jimulla 500 kenan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta nemi alfarma wajen Tinubu kan Aminu Ado Bayero

Ya ce wannan aikin wani bangare ne na kudirin Shugaba Tinubu a karkashin shirin 'gina biranen sabunta fata', wanda aka fara da gina gidaje 3,112 a Karsana, Abuja.

Ministan ya ce a kashi na farko na wannan shirin za a gina gidaje 50,000 a faɗim Najeriya, cewar rahoton Pulse.

"Za a gina gidaje tsakanin 500-1000 a kowane wuri da aka zaɓa a shiyyoyi shida na ƙasar nan da Abuja, yayin da sauran jihohi 30, za a gina masu gidaje 250 kowane," in ji Ɗangiwa.

Waye ya dawo da Aminu Ado Kano?

A wani rahoton kuma Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Ɗanagundi ya fayyace gaskiya kan yadda aka dawo da Aminu Ado Bayero cikin birnin Kano.

Ɗanagundi ya ce babu ruwan mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaron ƙasa, Malam Nuhu Ribadu a wannan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel