Jami'an Tsaro Sun Ɗauki Mataki da Majalisa Ta Fara Gyara Dokar Masarautun Kano
- An tsaurara matakan tsaro yayin da majalisar dokokin Kano ta fara zaman gyara dokar masarautu yau Laraba, 22 ga watan Mayu, 2024
- Shugaban masu rinjaye na majalisar kuma mamba mai wakiltar Dala, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ne ya gabatar da kudirin
- Tsohon gwamna, Dakta Abdullahi Ganduje ne ya fara rattaɓa hannu a dokar a 2019 kuma daga bisani aka tsige Sarkin Kano na 14
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Dakarun rundunar ƴan sanda da jami'an hukumar tsaron fararen hula NSCDC sun mamaye muhimman wurare a zauren majalisar dokokin jihar Kano.
An tsaurara matakan tsaron ne yayin da ƴan majalisar suka fara gyaran dokar masarautun jihar da ta kirkiro masarautu biyar a lokacin mulkin Abdullahi Ganduje.
Shugaban masu rinjaye na majalisa kuma mamba mai wakiltar Dala, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa, ne ya gabatar da kudirin yi wa dokar masarautu garambawul.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, kudirin gyara dokar masarautu (gyara na 2) ya shiga karatu na farko a majalisar dokokin Kano yau Laraba.
Yadda aka tsaurara matakan tsaro a Kano
Ƴan jaridar da suka je ɗauko rahoton zaman ƴan majalisa sun gamu da binciken kwaƙwaf kafin a bari su shiga zauren majalisar.
Haka nan kuma rahotanni sun nuna cewa an girke dakarun tsaro cikin shirin ko ta kwana a dukkan hanyoyin zuwa majalisar, Channels tv ta ruwaito.
Wani babban jami’in majalisar, wanda ba ya son a ambaci sunansa, ya ce babu wani abu komai girmansa da zai iya dakatar da wannan garambawul ga dokar.
Shirin gyara dokar masarautu a majalisae Kano
"Mun shirya wannan aiki tuntuni Allah ne kaɗai zai iya dakatar da wannan gyaran. Mun so ana rantsar da wannan gwamnatin zamu sauke waɗannan sarakunan.
"Gobe za a yi zama na musamman a majalisar dokoki domin gama karatu da kuma amincewa da gyaran dokar," in ji shi.
Yadda Ganduje ya tsige Sanusi II
Wannan dokar ce tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje ya yi amfani da ita wajen tsige Sarkin Sanusi Lamido Sanusi kuma ya ƙirƙiro masarautu biyar.
Ganduje ya fara rattaɓa hannu kan dokar ranar 5 ga watan Disamba, 2019 kuma ya sake sa hannu kan garambawul din da aka yi wa dokar a watan Oktoba, 2020.
An yi wa dokar masarautun garambawul ne bayan tsige Sanusi II ranar 9 ga watan Maris, 2020, inda dokar ta tanadi cewa, "shugaban majalisar sarakunan ya kasance Sarkin Kano.
Alhazan Kano za su fara tashi
A wani rahoton kun ji cewa yau za a fara jigilar alhazan jihohin Kano, Kaduna da wasu jihohin Arewa zuwa ƙasa mai tsarki bayan kammala kwashe na Nasarawa
Hukumar NAHCON ce ta bayyana haka a wata sanarwa da Fatima Sanda Usara, mai magana da yawun hukumar ta rattaɓawa hannu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng