Ministar Tinubu Ta Jawo An Fasa Ɗaura Auren Marayun Ƴan Mata 100 a Jihar Niger

Ministar Tinubu Ta Jawo An Fasa Ɗaura Auren Marayun Ƴan Mata 100 a Jihar Niger

  • Sakamakon kai shi ƙara kotu, kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Abdulmalik Sarkinɗaji ya soke shirin aurar da marayun ƴan mata 100
  • Sarkindaji ya bayyana cewa ya haƙura ya bar wa ministar harkokin mata ta ɗauki nauyinsu, inda ya ce ta wuce gona da iri kan lamarin
  • Ministar dai ta kai ƙarar kakakin majalisar gaban kotun saboda zai aurar da matan, ta nemi a dakatar da shi daga wannan aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Abdulamlik Sarkindaji, ya dakatar da shirin ɗaukar nauyin auren ‘yan mata marayu 100 a mazabarsa.

Kakakin majalisar ya bayyana cewa ya faɗa aurar da matan saboda abubuwan da suka biyo baya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka 50, sun sace mutane sama da 500 a Arewa

Shugaban majalisar Neja, Abdulmalik Sarkindaji.
Kakakin majalisar dokokin jihar Neja ya fasa ɗaukar nauyin aurar da marayun ƴan mata 100 a mazaɓarsa Hoto: Abdulmalik Sarkindaji
Asali: Facebook

Meyasa kakakin majalisar ya fasa auren?

Sarkindaji ya dauki wannan matakin ne biyo bayan matakin da ministar harkokin mata, Uju Ohannaya ta dauka na kai shi ƙara gaban kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministar matan ta kai ƙarar shugaban majalisar dokokin Neja gaban kotu ne domin ta dakatar da yunƙurinsa na yi wa ƴan mata 100 auren gata.

Honorabul Sarkindaji ya bayyana cewa a yanzu ya barwa ministar harkokin matan ta ɗauki nauyin aurar da marayun ƴan matan.

Ministar mata za ta aurar da marayu?

Shugaban majalisar ya faɗi haka ne ranar Talata yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya ce ministar ta wuce gona da iri.

A cewar Sarkindaji, tuni ya bayar da kudade ga iyayen ‘yan matan da za a ɗaura wa auren ta hannun sarakunan gargajiya da malaman addini na mazabar sa.

Ya kuma tabbatar da cewa ba zai buƙaci a dawo masa da kuɗaɗen da ya rabawa iyayen ƴan matan ba, ya bar masu halak malak, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta maka kakakin Majalisa a kotu kan shirin aurar da mata marayu 100

Abdulmalik ya kuma nuna cewa dalilinsa na shirin daukar nauyin daurin auren shi ne halin talauci da iyayen ‘yan matan ke ciki ba aikin mazaba ba kamar yadɗa yan jarida ke yaɗawa.

Gwamnatin Niger ta ɗauki mataki kan daba

A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Neja ta amince da jami'an tsaro su harbe duk dan dabar da su ka gani yawo da muggan makamai a jihar.

An dauki matakin ne a tarom masu ruwa da tsaki da ya gudana a fadar Sarkin Minna, Mai martaba Alhaji Umar Farouk Bahago.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262