'Yan Sanda Sun Bayyana Dalilin da Ya Sa Suka Mamaye Gidajen Ƴan Majalisu a Fatakwal

'Yan Sanda Sun Bayyana Dalilin da Ya Sa Suka Mamaye Gidajen Ƴan Majalisu a Fatakwal

  • Rundunar ƴan sanda ta yi ƙarin haske kan dalilin tura dakaru zuwa gidajen ƴan majalisu a Fatakwal, jihar Ribas
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP Grace Iringe-Koko, ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da tsaro a yankin
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka fara takun saƙa tsakanin ƴan majalisar dokokin da Gwamna Siminalayi Fubara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta bayyana dalilin da ya sa ta tura ‘yan sanda kusan 30 dauke da makamai da motocin sulƙe zuwa gidajen ‘yan majalisar dokokin jihar a Fatakwal.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa girke dakarun ƴan sanda a gidajen ƴan majalisun ya ƙara haifar da tashin hankalin siyasa a jihar.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya nuna babban kuskuren Tinubu kan harajin tsaron yanar gizo

Yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun bayyana abin da ya sa suka mamaye rukunin gidajen ƴan majalisa a Fatakwal Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ƴan sanda sun mamaye gidajen ne a daidai lokacin da rigima ta haɗa ƴan majalisun da Gwamna Siminalayi Fubara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin majalisar na tsagin Ministan Abuja, Martins Amaewhule, ya yi zargin cewa gwamnan na shirin rusa gidajen, zargin da gwamnan ya ƙaryata.

Gwamnan ya ziyarci rukunin gidajen ranar Larabar da ta gabata, inda ya shaida wa manema labarai cewa, ya je ne don tantance yanayin gidajen da nufin gyara.

A baya-bayan nan shugaban APC na rikon ƙwarya, Tony Okocha, ya buƙaci majalisar dokokin ta fara shirin tsige Gwamna Fubara.

Dalilin tura ƴan sanda wurin gidajen

Rundunar ‘yan sandan ta ce an tura jami’ai unguwar ƴan majalisar da nufin tabbatar da zaman lafiya, ba wai wata manufa ta nuna bangaranci ba.

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko ce ta bayyana haka a wata sanarwa ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Bakuwar cuta ta bulla a Zamfara, an rasa rayukan bayin Allah

Ta ce rundunar ƴan sandan ta ɗauki wannan matakim ne bisa la'akari da rigingimun siyasar da suka sake dawowa a jihar kwanan nan, rahoton Guardian.

"Mun kara tura jami'ai yankin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma daƙile duk yunƙurin taɗa zaune tsaye.
"Muna tabbatarwa al'umma cewa babu wani abun tashin hankali kuma su ci gaba da harkokin su na yau da kullum ba tare da fargabar komai ba."

- SP Grace Iringe-Koko.

Kotu ta kori ƴan majalisa 27

A wani rahoton kuma ƴan majalisa 27 da ke goyon bayan ministan Abuja sun shiga matsala yayin da rikicin siyasar jihar Ribas ya dawo ɗanye.

Babbar kotun jiha mai zama a Fatakwal ta hana ƴan majalisa 27 bayyana kansu a matsayin mambobin majalisar Ribas har sai ta yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel