Gwamna Fubara Ya Ɗauki Zafi, Ya Canza Wurin Zaman Majalisar Dokokin Jihar Ribas

Gwamna Fubara Ya Ɗauki Zafi, Ya Canza Wurin Zaman Majalisar Dokokin Jihar Ribas

  • Yayin da rikicin jihar Ribas ke ƙara tsananta, Gwamna Fubara ya canza wurin zaman majalisar dokokin jihar Ribas
  • A wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Disamba, 2023, gwamnan ya ce an ɗauke matakin ne saboda babu tsaro a zauren majalisar
  • Wannan na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan shugaban APC na jiha ya umurci ƴan majalisar da ke goyon bayan Wike su tsige Fubara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya amince da dokar sauya wurin zaman majalisar dokokin jihar zuwa gidan gwamnati da ke Fatakwal.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, wannan mataki na kunshe ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 14 da watan Disamba, 2023.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bayyana dalilin da ya sa suka mamaye gidajen ƴan majalisu a Fatakwal

Gwamna Fubara ya canza wa ƴan majalisa wurin zama.
Gwamna Sim Fubara ya zartar da dokar canza wurin zaman mambobin majalisar dokokin jihar Ribas Hoto: Rivers State House Of Assembly, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Takardar ta bayyana cewa an sauya wa yan majalisar wurin da za su riƙa zama ne saboda ƙona asalin zauren majalisar dokokin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɓata gari sun kona majalisar Rivers

Idan baku manta ba a watan Oktoba, wasu ɓata gari suka kutsa cikin zauren majalisa kuma suka banka mata wuta.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa ‘yan majalisar na shirin fara yunkurin tsige Fubara.

Daga bisani gwamnan ya kai ziyara zauren majalisar tare da wasu magoya bayansa, inda ya sha alwashin cewa cire shi ba abu ne mai sauƙi ba, Channels tv ta ruwaito.

Fubara ya canza wurin zaman majalisa

A cikin takardar sauya wurin zaman majalisar, Fubara ya ce babu tsaro a zauren majlisar yanzu kuma ya zama barazana ga rayuwar ‘yan majalisar da ma’aikatansu.

"Ni Siminalayi Fubara, gwamnan jihar Ribas, a wannan rana ta 30 ga watan Oktoba, 2023 na ba da umarnin dukkan wani zama da aikin majalisar dokoki ya koma ɗakin taron gidan gwamnati a Fatakwal na wucin gadi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe babban malamin Musulunci da wasu mutum 30 a Zamfara

"Na ba da wannan umarni duba da karfin ikon da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bani kuma majalisa ta koma gidan gwamnati har sai an gyara asalin zauran majalisar dokokin."

APC ta umurci a tsige Fubara

Rikicin siyasar Ribas ya dawo ɗanye bayan shugaban APC na jihar, Chief Tony Okocha,ya umurci ƴan majalisar da ke goyon bayan Wike su tsige Fubara.

Tsagin Fubara, waɗanda suka hakura bayan sulhun da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yi sun sake yunƙurowa, inda suka zaɓi sabon kakakin majalisa.

Kotu ɗauki mataki kan ƴan majalisar Rivers

A wani rahoton kuma Ƴan majalisa 27 da ke goyon bayan ministan Abuja sun shiga matsala yayin da rikicin siyasar jihar Ribas ya dawo ɗanye.

Babbar kotun jiha mai zama a Fatakwal ta hana ƴan majalisa 27 bayyana kansu a matsayin mambobin majalisar Ribas har sai ta yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262