Kuɗin Kamfe Na Neman Jefa Kwankwaso a Rami, Wasu Ƴan Arewa Sun Goyi Bayan Tsagin NNPP

Kuɗin Kamfe Na Neman Jefa Kwankwaso a Rami, Wasu Ƴan Arewa Sun Goyi Bayan Tsagin NNPP

  • Kungiyar NAN ta bayyana goyon baya ga ƙorafin da aka kai wa EFCC domin ta binciki jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso
  • Tun farko tsagin NNPP ya buƙaci EFCC ta taso Kwankwaso a gaba domin ya yi bayani kan yadda aka ɓatar da kuɗin kamfe
  • A cewar ƙungiyar NAN, ya kamata a riƙa tabbatar da gaskiya da rikon amana a jam'iyyu domin gina al'umma mai adalci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wata ƙungiyar wayar da kan al'umma a Arewacin Najeriya (NAN) ta nuna goyon bayanta ga kiran da wani tsagin jam'iyyar NNPP ya yi kan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso.

Ƙungiyar NAN ta bayyana goyon bayanta kan lamarin wanda tsagin NNPP ya buƙaci hukumar EFCC ta binciki Kwankwaso kan cin amanar jam'iyyar da satar kuɗin kamfe.

Kara karanta wannan

Ganduje da APC sun yi rashi, dubunnan mambobin jam'iyyar sun koma NNPP

Jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso.
Kungiyar NAN ta goyi bayan kira ga EFCC ta binciki Kwankwaso kan kuɗin NNPP Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

NAN da Rabiu Musa Kwankwaso

Shugaban NAN, Salihu Suleiman, ya bayyana wannan zargi da ake wa jagoran NNPP na ƙasa a matsayin babban lamarin da ya kamata a ɗauka da gaske.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada cewa ba wai kawai sun bayyana abin kunya ba ne, illa dai barazana ce ga mutuncin shugabannin siyasa na Arewacin Najeriya, rahoton Leadership.

Tsagin NNPP ya nemi a binciki Kwankwaso

Tun da farko tsagin NNPP, a cikin wata takardar koke da sakatare na kasa, Oginni Olaposi, ya shigar, ya yi zargin cewa an tafka magudi da sata a asusun jam’iyyar.

Mista Olaposi ya yi zargin cewa gaba ɗaya kuɗin da aka sayar da fam ɗin takara da wanda mambobi ke biya sun sulale kuma korarrun shugabannin NNPP ba su yi bayani ba.

Kwankwaso: NAN ta goyi bayan tsagin NNPP

Kara karanta wannan

"Yana da kyau amma...": Dattawan Arewa sun bayyana matsayarsu kan harajin CBN

Amma da yake martani kan haka, shugaban ƙungiyar NAN Sulaiman ya bayyana buƙatar a gudanar da tsaftataccen bincike kan wannan lamarin, cewar jaridar Independent.

Ya ce idan har zarge-zargen da ke cikin ƙorafin da aka miƙa wa EFCC kan Kwankwaso suka zama gaskiya, to ba shi kaɗai abin zai ɓata wa suna ba, gaba ɗaya Arewa zai taɓa.

Kungiyar ta yi kira da a tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin siyasa, inda ta jaddada cewa babu wani mutum duk girmansa da ya fi karfin doka.

“NAN tana goyon bayan tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma da’a a tsarin siyasarmu.
"Mun yi imanin cewa ta hanyar kiyaye wadannan ka’idoji ne kawai za mu iya gina ƙasa mai gaskiya da adalci ga daukacin ‘yan Nijeriya,” in ji Suleiman.

Sai dai wani jigon NNPP a Kano, Malam Sa'idu, ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan farfaganda ce ta bara gurbin jam'iyyar da ke neman suna.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi martani kan zargin neman cin hancin $150m a hannun Binance

"Ban yi mamaki ba domin wannan tsagin ne a baya ya fito ya sanar cewa ya kori mai gida, babu wanda ya sansu, burinsu kawai su jawo hankali a san da zaman su.
"Kwankwaso ya fi ƙarfin ya ci kuɗin kamfe, da kuɗinsa ya yi harkoki da dama na yaƙin neman zabensa kuma mu ma nan mun sanya namu. Na san EFCC ba za ta biye masu ba," in ji shi.

Yahaya Bello bai tsere ba

A wani rahoton na daban an musanta rahoton da ke yawo da hoto cewa Yahaya Bello ya sa kayan mata domin ya fice daga Najeriya

Bincike ya nuna hoton da ake yaɗawa da sunan Yahaya Bello ne ya yi shigar mata bayan EFCC ta fara nemansa ruwa a jallo ba na gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262