Kotu Ta Raba Gardama Kan Rikicin Shugabancin Jam'iyyar Labour Party

Kotu Ta Raba Gardama Kan Rikicin Shugabancin Jam'iyyar Labour Party

  • An tabbatar da Barista Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa bayan kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da hukuncin da ƙaramar kotu ta yanke
  • Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta yanke hukunci a kan Abure, inda ta buƙace shi da ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar
  • Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa babbar kotun ta yi kuskure wajen yanke hukuncin dakatar da Julius Abure

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar Labour Party (LP) na ƙasa, inda ta soke hukuncin da babbar kotun birnin tarayya Abuja ta yanke a baya.

Kara karanta wannan

Shugabannin majalisa za su gana da Shugaba Tinubu, bayanai sun fito

A shekarar da ta gabata ne dai babbar kotun babban birnin tarayya Abuja ta haramtawa Abure da wasu mutum biyu bayyana kansu a matsayin jami’an jam’iyyar na ƙasa, amma kotun ɗaukaka ƙara ta soke wannan hukuncin.

Kotu ta tabbatar da kujerar Julius Abure
Kotu ta tabbatar da Abure a matsayin shugaban LP Hoto: Labour Party
Asali: Facebook

A shekarar da ta gabata ne mai shari’a Hamza Muazu daga babban kotun Abuja, ya bayar da umarnin wucin gadi inda ya umurci Abure da wasu jami’ai biyu da su daina aiki a matsayin shugabannin jam’iyyar saboda zarge-zargen da ake yi musu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kotun ɗaukaka ƙara ta soke wannan hukuncin, cewar rahoton jaridar The Nation.

Wane hukunci kotun ta yanke?

A hukuncin da mai shari’a Hamma Barka ta yanke, kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da cewa babbar kotun ta yi kuskure wajen sauraron shari’ar, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Kotun daukaka ƙarar ta yanke hukuncin cewa Lamidi Apapa ya biya diyyar N1m ga Julius Abure.

Kara karanta wannan

Babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan bidiyon 'Dalan' tsohon gwamnan Kano Ganduje

Wannan matakin samo asali ne daga takaddamar shari'a da aka daɗe a na yi a tsakanin Abure da Apapa, wacce ta fara tun kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Wannan rigimar ta sa jam’iyyar LP ta rabu gida biyu, wanda kusan hakan ya shafi sakamakon zaɓen fidda gwanin da ya haifar da Peter Obi.

Sabon Rikici Ya Ɓarke a Jam'iyyar LP

A baya rahoto ya zo cewa an samu ɓarkewar sabon rikici a jam'iyyar Labour Party (LP), bayan da mai ajiyar kuɗi ta jam'iyyar ta zargi Julius Abure da karkatar da N3.5bn.

Misis Oluchi Opara na zargin shugaban jam'iyyar ne da laifin karkatar da kuɗaɗen waɗanda aka samu lokacin yaƙin neman zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng