'Yan Majalisa 16 Sun Shiga Matsala 1 Kan Yunƙurin Tsige Shugaban Majalisar Dokoki a Arewa

'Yan Majalisa 16 Sun Shiga Matsala 1 Kan Yunƙurin Tsige Shugaban Majalisar Dokoki a Arewa

  • Mambobi 16 daga cikin 24 na majalisar dokokin jihar Zamfara sun shiga matsala kan yunƙurin tsige shugaban majalisar, Bilyaminu Moriki
  • A zaman ranar Litinin, ƴan majalisa 7 suka sanar da dakatar da abokan aikinsu 16 kan abinda suka aikta ranar Alhamis a makon da ya gabata
  • Sun kuma jaddada cewa Moriki na nan daram a matsayinsa na shugaban majalisar tare da rokon al'umma su yi watsi da batun dakatar da shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Ga dukkan alamu rikici ya raba kawunan mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya kan batun tsaro.

A zaman yau Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2024, bakwai daga cikin mambobi 24 na majalisar sun sanar da dakatar da ƴan majalisa 16 daga aiki.

Kara karanta wannan

An tsige kakakin majalisa a wata jihar Arewa saboda babban dalili 1

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara.
An dakatar da yan majalisu 16 kan yunkurin tsige kakakin majalisar dokokin Zamfara Hoto: Bilyaminu Moriki
Asali: Facebook

Channels tv ta tattaro cewa an dakatar da ƴan majalisa 16 ne saboda yunƙurin da suka yi na tsige shugaban majalisar dokokin Zamfara, Bilyaminu Moriki, ranar Alhamis da ta wuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun zargi waɗanda matakin dakatarwan ya shafa da kutsa kai ofishin magatakardan majalisa tare da lalata muhimman abubuwa a harabar majalalisa.

Majalisa karƙashin jagorancin Bilyaminu Moriki ta ayyana zaman da mambobi 18 suka yi ranar Alhamis da ta gaba a matsayin wanda ya saɓa doka.

Ina aka kwana kan dakatar da kakakin majalisar Zamfara?

Haka zalika ƴan majalisar sun yi kira ga mazauna jihar da su yi watsi da labarin da ake yadawa cewa an dakatar da shugaban majalisar, Vanguard ta rahoto.

Sun kuma zargi wasu manyan ‘yan siyasa da ke wajen jihar da daukar nauyin ‘yan majalisar domin kawo cikas ga gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Dakarun noma: Gwamnati ta dauki mataki 1 na tsare manoma daga farmakin 'yan bindiga

Abinda ya haddasa taƙaddama a majalisar tun farko

Idan baku manta ba a ranar Alhamis ɗin makon jiya, mambobi 18 suka dakatar da Moriki daga matsayin shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara.

A cewarsu, sun ɗauki wannan matakin ne saboda shafe tsawon lokaci ba a ji ɗuriyarsa a majalisar ba duk da halin da ake ciki na karuwar hare-haren ƴan bindiga.

Gwamna Lawal ya ziyarci kauyuka 2

A wani rahoton kuma Gwamna Dauda Lawal ya kai ziyara ta musamman yankunan da ƴan bindiga suka kai hari a kananan hukumomin Zurmi da Birnin Magaji a Zamfara.

Yayin wannan ziyara, gwamnan ya yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da jaddada shirin gwamnati na dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262