Babbar Ƙotu Ta Yanke Hukunci Kan Buƙatar Magoya Bayan Gwamnan PDP da Ake Zargi da Ta'addanci

Babbar Ƙotu Ta Yanke Hukunci Kan Buƙatar Magoya Bayan Gwamnan PDP da Ake Zargi da Ta'addanci

  • Babbar kotun tarayya ta yi hukunci kan buƙatar belin magoya bayan Gwamna Fubara na jihar Ribas kan tuhumar ta'addanci
  • Mutanen 5 da aka kama na fuskantar shari'a kan tuhume-tuhume bakwai da suka samo asali daga ƙona wani sashin majalisar dokokin Ribas
  • Sufetan yan sanda na kasa ne ya shigar da tuhume-tuhume kan waɗanda ake zargi, masu biyayya ga Fubara a lokacin rikicin Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja -Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ranar Litinin, ta ƙi bayar da belin wasu mutane biyar da ake zargi da kai hari, barna da ƙona sashin majalisar dokokin Ribas.

Kamar yadda jaridar The Nation ta tattaro, waɗanda ake zargin sun haɗa da Chime Eguma Ezebalike, Prince Lukman Oladele, Kenneth Goodluck Kpasa, Osiga Donald da Ochueja Thankgod.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun kai farmaki wurin taron murnar nasarar gwamnan PDP a Kotun Ƙoli, sun tafka ɓarna

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara.
Kotu Ta Yi Fatali da Bukatar Belin Magoya Bayan Gwamna Fubara 5 Kan Zargi Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Wane laifuka ake zarginsu da aikatawa?

Babban Sufetan ƴan sanda na ƙasa ne ya gurfanar da su a gaban ƙuliya kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi ta'addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ƴan sanda ƙarƙashin IGP ta zargi waɗanda ake tuhuma da cewa a lokacin da danbarwar siyasar jihar Ribas ta yi ƙamari, sun kai farmaki zauren majalisar dokoki.

A cewar rundunar, sun yi haka ne da nufin kawo cikas a yunkurin da ƴan majalisa suka yi na tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan karagar mulki.

Bayan haka, a ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CR/25/2024, ana tuhumar su da laifin kashe wani Sufeton ‘yan sanda, SP, Bako Agbashim, da wasu ‘yan sanda biyar a Ahoada da ke jihar Ribas.

Yadda aka fafata kan buƙatar neman beli

Sai dai wadanda ake kara ta bakin lauyoyinsu sun roki kotun da ta bada belinsu har zuwa lokacin da za a yanke hukunci a shari'ar.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake yin martani mai zafi ga Atiku kan abu 1 tak

Sun shaida wa kotun cewa bisa tanadin kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa garambawul, su ba masu laifi bane har sai an tabbatar da laifinsu.

A na shi ɓangaren, lauyan ‘yan sanda, Mista Simon Lough, SAN, ya nuna cewa wadanda ake tuhumar ba su da wata hujja mai ƙarfi da zata sa a sake su da sunan beli.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tuhumar da ake yi wa mutanen ya kunshi manyan laifuka. Maimakon haka, ta bukaci kotu da ta ba da umarnin a hanzarta shari'ar wadanda ake kara.

Wane hukunci kotu ta yanke?

A hukuncin da ta yanke a ranar Litinin, mai shari’a Bolaji Olajuwon, ta amince da bayanin masu kara, ta kuma yi watsi da bukatar belin waɗanda ake tuhuma, rahoton Vanguard.

Sanata Sani ya caccaki tsohon shugaban kasa

A wani rahoton na daban Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana dalilin da yasa Bola Tinubu ke shan wahala a kokarin saita Najeriya.

Sanata Sani ya jaddada cewa tsohuwar gwamnati ƙarƙashin Muhammadu Buhari ta bar gadon tulin bashi ga gwamnati mai ci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262