INEC ta ayyana Shittu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben raba gardama na majalisa ta Oyo
- Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa (INEC) ta ayyana Shittu Ibrahim a matsayin wanda ya zabe zaben raba gardama na dan majalisar mazabar Saki ta Yamma a jihar Oyo
- Dan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya doke Jullius Okedoyin na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP)
- Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin kotun zabe ta kuma umurci a yi zaben raba gardama a akwatunan zabe biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Saki, Jihar Oyo - An ayyana dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Shittu Ibrahim, a matsayin wanda ya lashe zaben raba gardama da aka yi na Saki ta Yamma a jihar Oyo.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa (INEC) ta ayyana Shittu a matsayin wanda ya lashe zaben ya doke mai biye masa, Julius Okedoyin, na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar The Nation, Shittu na samu kuri'u 290 yayin da Okedoyin ya samu kuri'u 330 a ranar Asabar 3 ga watan Fabrairu.
Dan takarar na APC ya samu kuri'u 200 a guduma ta 7, 6 a Odo Osun ya samu doke Okedoyin, wanda ya samu kuri'u 190.
Jami'in kula da zabe na INEC ya ce APC ta samu kuri'u 13,982 a gunduma biyu yayin da PDP ta samu kuri'u 13,755. Jam'iyyun biyu sun samu kuri'u 299 da 333 bayan sakamakonsu na farko, New Telegraph ta rahoto.
Bayan ayyana sakamakon, dan takarar na APC ya doke Femi Julius na PDP a mazabar ta jihar.
A Nuwamban 2023, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin kotun zabe ta umurci a yi zaben raba gardama.
Kotun Daukaka Karar kuma ta umurci INEC ta karbe takardan shaidan cin zabe daga Shittu.
Asali: Legit.ng