Gwamnan PDP Ya Dakatar da Kwamishina 1 da Wasu Manyan Jiga-Jigan Gwamnati Kan Abu 1 Tal

Gwamnan PDP Ya Dakatar da Kwamishina 1 da Wasu Manyan Jiga-Jigan Gwamnati Kan Abu 1 Tal

  • Gwamnan jihar Delta ya dakatar da kwamishinan noma da albarkatun ƙasa, Omoun Perez, tare da wasu manyan jami'ai a ma'aikatarsa
  • Sherrif Oborevwori ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin baiwa kwamitin binciken damar gudanar da aikinsu ba tare da samun tsaiko ba
  • Ya kuma tabbatarwa al'ummar jihar cewa gwamnatinsa zata kammala dukkan ayyukan da ta taras kuma ta kawo sabbi domim ci gaban Delta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya ba da umarnin dakatar da kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar, Omoun Perez, nan take.

Baya ga haka, gwamnan ya umarci babban sakataren ma'aikatar noma, Bennett Agamah; mataimakin darakta, Oki Yintareke, babban akanta, "su tafi hutun dole har sai baba ta gani."

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki yayin da almajiri da mai gadin makaranta suka dauki ransu a Kano

Gwamnan jihar Delta, Sherrif Oborevwori.
Gwamnan Jihar Delta Ya Dakatar da Kwamishina da Wasu Hadimai Daga Aiki Hoto: Sherrif Oborevwori
Asali: Facebook

Wannan mataki na kunshe a wata sanarwa da sakataren gwamnatin Delta, Dakta Kingsley Emu, ya fitar kuma aka raba kwafi ga manema labarai a Warri ranar Laraba, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnan ya ɗauki wannan mataki?

Sanarwan ta nuna cewa dakatar da waɗannan mutanen ya zama tilas bayan nazari kan rahoton yadda ma'aikatar noma ta aiwatar da aikin Greenhouse.

Ta kara da cewa an dauki matakin ne bayan samun rahoton wucin gadi na kwamitin da kuma samar da damar tattara bayanai ba tare da wani cikas ba a lokacin gudanar da bincike.

Kamar yadda Daily Post ta tattaro, wani sashin sanarwan ya ce:

"Gwamna Oborevwori ya kafa kwamitin mutum 7 karkashin sakataren gwamnatin jihar domin gudanar da bincike kan zargin da ake da yadda aka samu sabani a aiwatar da aikin na ma’aikatar.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fara shirin murabus daga muƙaminsa don yin takara? Gaskiya ta bayyana

"Matakin da gwamnati ta ɗauka ba yana nufin sun yi laifi bane face don tabbatar da an yi bincike mai tsafta ba tare da nuna son kai ko samun wani cikas ba."

Oborevwori ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar bin ba'asi da tabbatar da an kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa a fadin jihar.

Ya kuma yi alkawarin ƙirƙiro wasu sabbin ayyuka domin dorewar ci gaban jihar, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Festus Ahon ya fitar.

Majalisa ta amince da tsige Oluomo a jihar Ogun

A wani rahoton na daban kun ji cewa matakin tsige kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo, na nan daram.

Ƴan majalisa 22 da suka halarci zaman yau Talata sun kaɗa kuri'ar amincewa da tsige shi bayan gabatar da rahoton bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262