Shugaban Majalisar Dokokin Jihar da Aka Tsige Ya Ɗau Zafi, Ya Ce Yana Nan Daram a Kujerarsa

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar da Aka Tsige Ya Ɗau Zafi, Ya Ce Yana Nan Daram a Kujerarsa

  • Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Kunle Oluomo, ya fusata da matakin abokan aikinsa na tsige shi daga kan muƙamin
  • Da yake martani kan lamarin ranar Jumu'a a gidansa, Oluomo ya ce yana nan daram a matsayin shugaban majalisar jihar Ogun
  • Ya kuma sanar da cewa tuni ya garzaya ya kai ƙara gaban kotu kan tsige shi da aka yi wanda ya kira da haramun a tsarin dokar ƙasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Rigingimun da suka dabaibaye majalisar dokokin jihar Ondo bayan tsige kakakin majalisar sun ɗauki sabon salo a daren ranar Jumu'a, 26 ga watan Janairu.

Tsohon kakakin majalisar dokokin wanda abokan aikinsa suka tsige daga muƙamin, Honorabul Kunle Oluomo, ya ce yana nan daram a kujerar shugaban majalisar.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar jihar APC da aka tsige ya nufi kotu

Tsigaggen kakakin majalisar jihar Ogun, Kunle Oluomo.
Ina nan a matsayina na shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, in ji Oluomo Hoto - Kunle Oluomo
Asali: UGC

Honorabul Oluomo, wanda ke wakiltar mazaɓar Ifo 1 ya yi bankwana da kujerar shugaban majalisar dokokin jihar Ogun ne ranar Talata da ta gabata, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro muku cewa mambobi 18 na majalisar ne suka haɗu suka tsige Oluomo daga kan kujerar shugabancin kan zargin wadaƙa da kuɗaɗensu.

Nan take ba su ɓata lokaci ba suka zaɓi Honorabul Oludaisi Elemide a matsayin sabon kakakin majalisar wanda ya maye gurbinsa.

Oluomo ya mayar da martani kan tsige shi

Amma kwanaki uku bayan faruwar wannan lamari, tsohon kakakin ya fito ya yi magana kan taƙaddamar da ta kai ga raba shi da muƙamin shugabancin majalisar Ogun.

Ya ayyana matakin da ƴan majalisa 18 suka ɗauka na tsige shi a matsayin, "saɓawa kundin tsarin mulki, mara amfani kuma wanda ba zai yi tasiri ba ko kaɗan."

Kara karanta wannan

Rundunar Soji ta tona asirin mutum 2 da ƙarin wasu abubuwa da suka jawo kashe-kashe a Filato

Mista Oluomo ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a gidansa da ke rukunin gidajen ƴan majalisu a Ibara GRA a Abeokuta, babban birnin Ogun ranar Jumu'a.

Ya kuma ƙara da bayanin cewa tuni ya shigar da ƙara a gaban kotu domin kalubalantar matakin tsige shi, rahoton Daily Trust.

Fubara ya rantsar da kwamishinoni 9

A wani rahoton kuma Gwamna Fubara ya sake rantsar da kwamishinoni 9 karo na biyu a wani biki da aka shirya a gidan gwamnatinsa da je Fatakwal.

Kwamishinonin sun yi murabus a farko domin nuna goyon bayansu ga Wike, amma daga bisani gwamnna ya sake naɗa su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262